Hukumomi a Benin sun bayyana cewa yankin arewacin ƙasar da aka kashe sojojin a ranar 5 ga watan Yunin 2024 na yawan fama da barazanar masu tayar da kayar baya./ Hoto: Reuters      

Wasu 'yan bindiga sun kashe sojojin ƙasar Benin bakwai a wani hari da suka kai wurin yawon buɗe ido na Pendjari da ke arewacin ƙasar kusa da kan iyaka da Burkina Faso, a cewar majiyoyin tsaro a ranar Laraba.

Majiyoyin dai ba su bayyana ko su wane ne ba, amma harin na ranar Talata shi ne na baya-bayan da aka kai yankin da ke kan iyaka da Benin wanda ke yawan fama matsalar masu tayar da ƙayar baya a yankin Sahel da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma masu fasa-ƙwauri.

“An tabbatar da labarin mutuwar ‘yan'uwanmu sojoji guda bakwai,” kamar yadda wata majiyar soji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, a yayin da take amsa tambayoyi game da harin.

Kazalika wata majiyar tsaro ta daban ta tabbatar da aukuwar harin.

Ƙokarin daƙile matsalar

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin kuma rundunar sojin ƙasar ba ta ce uffan a hukumance ba.

Ƙasashen yammacin Afirka da ke gaɓar tekun Guinea da suka haɗa da Benin da Togo da Ghana da kuma Cote d'Ivoire suna ƙoƙarin daƙile matsalar 'yan ta'adda wadda ta mamaye faɗin yankin Sahel da ke kan iyakokin arewacin ƙasashensu.

Ƙasar Benin dai tana iyaka da Burkina Faso da Nijar, inda ƙungiyoyin 'yan ta'adda suke yawan ta da zaune-tsaye.

A watan Mayu ne, sojojin Benin suka kashe wasu da ake zargin ‘yan ta'adda ne su 8 a arewa maso gabashin ƙasar da ke kusa da iyaka da Nijar.

Ƙarfafa tsaro

Juyin mulkin da aka yi a Nijar a watan Yulin bara ya yi sanadin janye sojojin Faransa da ke ƙasar, lamarin da ya ƙara sanya fargaba kan sake taɓarɓarewar tsaro a yankin Sahel.

Hukumomin ƙasar Benin sun aike da dakaru 3,000 domin daƙile barazanar tsaro a iyakar a wani shirin na Operation Mirador.

Ƙungiyar Tarayyar Turai EU ta ce za ta bayar da Euro miliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 54 domin taimaka wa sojojin ƙasar Benin wajen yaƙin da suke yi da ta'addanci musamman wajen samar musu da jiragen leƙen asiri da marasa matuƙa.

Ba kasafai gwamnatin Benin ke yin tsokaci game da tashe-tashen hankula a kan iyakokinta ba, amma jami'an ƙasar sun tabbatar da cewa tun daga shekarar 2021 zuwa yanzu sun fatata a manyan hare-hare kusan 20.

Tashin hankali kan iyaka

A watan Mayun shekarar 2019, an yi garkuwa da wasu Faransawa biyu a cikin motar yawon buɗe ido na gandun daji da ke Pendjari a yankin arewacin Benin, kana yana da nisan kilomita 5,000 (mil 3,100) da iyakar ƙasar da Burkina Faso.

'Yan ta'addan dai sun kashe jagoran da ya yi wa Faransawan rakiya wani ɗan ƙasar Benin, bayan mako guda ne dakarun Faransa sun yi nasarar kuɓutar da mutane biyun, tare da wani ɗan Koriya ta Kudu da wani Ba'amurke waɗanda aka yi garkuwa da su har tsawon kwanaki 28.

Sojojin Faransa biyu sun mutu a yayin farmakin.

Kazalika iyakar Benin da Nijar na fuskantar tashe-tashen hankula, inda a bangaren Nijar din har yanzu iyakar na rufe.

Harin 'yan ta'adda

Shugaban Patrice Talon na ƙasar Benin ya bukaci mahukunta a Nijar da su ba da haɗin kai domin a sake buɗe iyakar.

A wani rahoton tsaro da ta fitar, gwamnatin ƙasar Togo da ke makwabtaka da Benin ta ce mutane sama da 30 sun mutu a bara sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda a arewacin ƙasar

Kazalika a bara ne shugaba Faure Gnassingbe ya ce 'yan ta'adda sun kashe mutane 140, ciki har da fararen-hula kusan dari, tun bayan harin farko da suka kai a ƙarshen shekarar 2021.

AFP