Manyan ƙungiyoyi guda biyu na ƙwadago a Nijeriya sun yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu su aiwatar da sabon tsarin albashi wanda aka riga aka amince da shi ga ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Wasu daga cikin ma'aikatan gwamnati miliya 1.2 sun fara samun ƙarin albashin da aka ƙayyade mafi ƙaranci kan naira 70,000 (dala $42) duk wata, ƙarƙashin sabon tsarin.
Ƙaddamar da sabon mafi ƙarancin albashin ya fara wannan makon, amma wasu ma'aikatan suna ganin ƙarin bai isa ya magance ƙalubalen tattalin arziƙin da suke fuskanta ba, bayan shugaba Bola Tinubu ya kafa dokar sabon tsarin a ƙarshen Yuli.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa Joe Ajaero, ya ce tayin albashin N70,000 an karɓe shi ne saboda an amince cewa za a dinga sauya fasalin albashi duk bayan shekara uku.
'Bin na gaba'
A halin yanzu Nijeriya na fama da mummunan matsin tattalin arziƙi, wanda ya haifar da rasa matsayinta na wanda ta fi girman tattalin arziƙi a Afirka. Hauhawar farashi da tsarin musayar kuɗin ƙasashen waje mara tabbas, sun taimaka wajen tsanantar matsin rayuwa ga al'ummar ƙasar miliyan 200.
Bayan aiwatar da sabo tsarin albashin, Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa ta nemi kamfanoni da ƙungiyoyi masu zaman kansu su gaggauta fara aiki da sabon tsarin albashin kan ma'aikatansu.
Benson Upah, kakakin Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, da Tommy Etim, mataimakin shugaban ƙungiyar Trade Union Congress, sun nemi kamfanoni su yi ƙarin albashi.
"Muna ƙarfafa cewa kamfanoni masu zaman kansu su bi na gaba," Upah ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
'Babu dalilin jinkiri'
"Kwamitin gwamnatin tarayya kan daidaita albashi ya riga ya samar da jadawali, don haka babu wani karɓaɓɓen dalilin jinkiri daga kamfanoni wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi,” in ji Etim.
“Muna kausasa kira da duka ɓangarori su bi wannan tsari su fara biyan sabon albashi,'' a cewar shugaban na ƙwadago.
Sai dai wata ma'aikaciyar gwamnati, Josephine Isiah ta bayyana rashin gamsuwa kan sauyin, inda ta ce ƙarin bai isa ba ganin munin matsin tattalin arziƙi sakamakon tsare-tsaren gwamnati.
Ta faɗa wa Anadolu cewa, "Farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje ya tashi, inda ya haifar da hauhawar farashi da ƙarancin magunguna da wasu kayan masarufi".