Rahoton masana’antar mai da iskar gas, wanda aka gabatar ranar Juma’a a Abuja, ya bayyana yadda aka kashe dala biliyan 6.071 da kuma naira biliyan 66.4 na wasu kudaden kamasho da ba a biya ba, da kuma tarar hukuncin ƙona iskar gas da Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ke bi tun daga ranar 31 ga Agustan 2024.
Bugu da ƙari, akwai fitattun harajin ribar man fetur da harajin kudin shiga na kamfani, da kuma VAT da Hukumar Tara Harajin ta Tarayya (FIRS) ke bi wanda ya kai dala miliyan 21.926 da naira miliyan 492.8 daga watan Yunin 2024.
Rahoton na hukumar NEITI ya kuma bayyana yadda aka samu faduwar kashi 9 cikin 100 na kudaden shiga na masana'antar a shekarar 2023, inda aka samu dala biliyan 16.467 idan aka kwatanta da dala biliyan 18.106 a shekarar 2022.
Rahoton NEITI ya bayyana cewa an yi asarar gangar danyen mai miliyan 7.68 a shekarar 2023 sakamakon sata da kurakuran da aka samu wajen aunawa, inda hakan ya jawo samun raguwar kashi 79 cikin 100 daga ganga miliyan 36.69 da aka yi asara a shekarar 2022.
Bugu da ƙari, an jinkirta haƙo ganga miliyan 153.44 na ɗanyen mai a shekarar 2023, kamfanoni irin su SPDC (ganga miliyan 39.13) da TEPNG (ganga miliyan 6.07), da TUPNI (ganga miliyan 3.5) ne suka fi fuskantar matsalar.
Rahoton ya bayyana cewa gwamnati ta biya naira tiriliyan 3.01 a matsayin tallafin mai a shekarar 2023 idan aka kwatanta da naira tiriliyan 4.71 da aka biya a shekarar 2022.
Ya bayyana cewa an shigo da jimillar lita biliyan 23.54 na tataccen man fetur zuwa cikin kasar nan a shekarar 2022, yayin da aka shigo da lita biliyan 20.28 a shekarar 2023. Wannan yana nuna raguwar lita biliyan 3.25, ko kuma raguwar kashi 14 cikin 100, sakamakon cire tallafi.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rahoton, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa gwamnati za ta ci gaba da bai wa NEITI ‘yancin cika aikinta ga kasar nan da kuma cibiyar bin diddigin masana’antu ta duniya, EITI.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Olanipekun Olukayode, ya yi alkawarin yin amfani da sabon rahoton da aka fitar don tabbatar da cewa gwamnati ta ƙwato duk wasu makudan kudaden haraji da ake bin kamfanonin.
Shugaban hukumar ya sanar da cewa daga rahotannin da hukumar NEITI ta fitar a baya-bayan nan, EFCC ta kwato tare da tura sama da naira biliyan ɗaya zuwa asusun gwamnatin tarayya.