Mutane 17 sun rasa rayukansu a wasu harbe-harbe a wani gari Afirka ta Kudu 'yan awanni tsakaninsu a gundumar Eastern Cape.
'Yan sanda sun ce sun ƙaddamar da farautar maharan bayan faruwar harin a ƙauyen Ngobozana na garin Lusikisiki.
"A gida guda an kashe mutane 13, ciki har da mata 12 da namiji guda. A wani gidan kuma, an kashe mutum huɗu. Mutum na 18 yana cikin mummunan hali a asibiti," in ji 'yan sanda a wata sanarwa ta shafin X.
Hari na farko ya faru ne ranar Juma'a, sai ɗayan kuma a awannin safiyar Asabar, cewar kakakin 'yan sanda Brigadier Athlenda Mathe, kamar yadda jaridun yankin suka ambato shi.
Ministan 'yan sanda Senzo Mchunu da kwamishinan 'yan sanda na ƙasa General Fannie Masemola za su gabatar da jawabi ga 'yan jarida kan harbe-harben, a tsakiyar ranar Asabar.