Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce kimanin mutane miliyan biyu ne har yanzu ke rayuwa ba a gidajensu ba, sakamakon fitar da su da mummunar ambaliyar ruwa ta yi a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Babagana Zulum ya ce wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta ranar 10-11 ga Satumba ta shafa na ci gaba da zama a sansanonin ‘yan gudun hijira da gwamnati ta kafa sakamakon bala’in.
“Yawancin mutanenmu har yanzu suna gudun hijira kuma ambaliyar ta lalata yawancin ababen more rayuwa,” kamar yadda Zulum ya shaida wa jami’ai na wani bankin Najeriya, wanda ya ba da gudummawar Naira biliyan daya don gyara ababen more rayuwa da ambaliyar ta lalata da kuma tsugunar da wadanda ambaliyar ta raba da mahallansu.
Zulum ya yi alkawarin cewa za a yi amfani da duk gudummawar da ke cikin asusun tallafin ambaliyar ga wadanda abin ya shafa, ba jami’ai ne za su karkatar da su ba.
Dubban mutane ne ke fakewa a waje, da cibiyoyin addini, da sansanonin 'yan gudun hijira 32 da suka hada da makarantun gwamnati, tun bayan mummunar ambaliyar ruwan, wacce ta kashe akalla mutane 40.
Hukumomin yankin sun fara rabon kudi da abinci da sauran kayan buƙatu ga wadanda ke sansanonin da wasu kadan da ke fakewa a wuraren da ba bu wata matsala.
Bulana Abiso, shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hula, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Anadolu cewa har yanzu harkokin tattalin arziki ba su koma kamar da ba a birnin, tun bayan ambaliyar.
Abiso ya ce har yanzu yawancin wadanda abin ya shafa na cikin kaduwa kuma suna fatan ganin sun shawo kan kaduwar da suka yi saboda hasarar da suka yi, sannan suna so ga yadda za su kawo karshen zaman da suke yi a sansanonin masu neman mafaka sakamakon ambaliyar.
Cibiyoyi da daidaikun jama’a, sun ba da gudummawar kudi don tallafa wa wadanda abin ya shafa.