Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da 'yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF ta ce mayakan kungiyar 17 da iyalansu 45 ne suka yi saranda.
Rundunar ta bayyana haka ne a sanarwar da kakakinta Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar ranar Asabar.
“A cikin kwanaki biyu, tsakanin 14 zuwa 15 ga Agustan 2023, manyan kwamandojin Boko Haram hudu da mayaka 13 da iyalansu 45 suka ajiye makamansu tare da saranda ga dakarun runduna ta uku ta MNJTF da ke Cross Kauwa da Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa a Nijeriya.
“Kayayyakin da suka yi sarandarsu sun hada da AK-47 biyu da bindigar FN (SLR) daya da kuma kusan harsasai 440 na bindigogi daban-daban da sauran kayayyaki masu muhimmanci na ‘yan tawaye,” in ji sanarwar.
A ranar da suka soma sarandar a ranar 14 ga watan Agustar 2023, kwamandojin Boko Haram biyu ne suka soma mika wuya da mayakansu tara da iyalansu 21.
Rundunar ta ce sun bayar da makamansu da suka hada da AK 47 shida da bindiga kirar FN (SLR) daya da jigida 20 cike da harsasai, da harsasai 12 nau’in 5.6 millimeter da gurnetin hannu daya da Bandolier uku da harsasai 180 nau’in 7.62 da sauran abubuwa.
Sannan rundunar ta bayyana cewa a rana ta biyu wato 15 ga watan Agusta, kwamandoji biyu da mayakansu hudu da iyalansu 24 suka amshi kiran sulhu inda suka yi saranda.
Su kuma sun mika AK-47 biyu da harsasai 99 nau’in 7.62 millimeter da rediyo biyu da kuma kudi naira 213,800 da sauran kayayyaki.