Kungiyar Boko Haram ta saki mata 49 da ta sace a Borno

Kungiyar Boko Haram ta saki mata 49 da ta sace a Borno

An sace matan ne ranar Talata a yayin da suka je yin itace a Shuwaei Kawuri.
Boko Haram ta kwashe shekara da shekaru tana kai hare-hare a jihar ta Borno da wasu yankunan Tafkin Chadi, inda ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu./Hoto: Reuters

Kungiyar Boko Haram ta saki mata arba’in da tara da mayakanta suka sace a farkon makon nan a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

An saki matan ne ranar Juma’a bayan wani jami’in gwamnati ya biya kudin fansa, a cewar biyu daga cikin wadanda aka saka da kuma wani jami’i.

An sace matan ne ranar Talata a yayin da suka je yin itace a Shuwaei Kawuri da ke wajen Maiduguri, in ji biyu daga cikin wadanda aka sako a hirarsu da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

"An saki dukkanmu ne da tsakar dare bayan mayakan Boko Haram sun shaida mana cewa ‘yan uwanmu sun biya musu bukatunsu," a cewar daya daga cikin matan.

Mayakan Boko Haram sun bukaci a biya su naira miliyan uku don su saki matan sai dai an biya naira miliyan daya don sakin wadannan matan, wadanda galibinsu kananan manoma ne, a cewar wani shugaban yankin.

Ya ce ba ya so a fadi sunansa. Kwamishinan matasa na borno da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sani Kamilu Shatambaya ba su bayar da amsa kan neman karin haske game da batun ba.

Ranar 1 ga watan Yuli, mayakan Boko Haran sun fille kawunan manoma 10 a jihar ta Borno a wani hari da suka kai.

Boko Haram ta kwashe shekara da shekaru tana kai hare-hare a jihar ta Borno da wasu yankunan Tafkin Chadi, inda ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.

Reuters