Kungiyar Boko Haram Ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi da muhallansu - inda dubbai suka yi kaura zuwa makwabtan kasashe - tun da ta soma kai hare-hare a 2002./Hoto: Reuters

'Yan ta'adda na kungiyar Boko Haram sun yanka manoma akalla 10 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya bayan sun kai musu hari, kamar yadda mazauna wani kauye suka bayyana ranar Litinin.

Daya daga cikin manoman da suka tsira daga harin, Abubakar Masta, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan ta'adda da ke kan babura dauke da bindigogi sun kai musu hari yayin da suke aiki a gonakinsu da ke kauyen Kawuri na karamar hukumar Konduga ranar Litinin da misalin karfe 08:30 na safe.

"Na ga gawarwaki 10 na abokaina da aka yanka," in ji Abubakar, a yayin da jami'an tsaro suke debo gawarwakin mutanen da lamarin ya shafa.

Mazauna kauyen sun ce 'yan Boko Haram ne suke da alhakin wannan danyen-aiki.

Wani mazaunin kauyen, Alkali Mommodu, ya ce yana cikin wadanda suka taimaka wa sojoji wurin gano gawarwarkin mutum 10 da aka yanka.

Kakakin 'yan sandan jihar bai amsa kiran wayar da aka yi masa domin yin karin haske game da harin ba.

A makon jiya, 'yan Boko Haram sun kashe akalla mutum 25 sannan suka jikkata mutane da dama a hare-haren da suka kai kauyuka biyu a jihar ta Borno.

Boko Haram na yawan kai hare-hare kan manoma da mazauna cikin garuruwa inda a wasu lokutan take bayar da umarni a daina noma lamarin da kan sa farashin kayan abinci ya yi matukar tashi a yankunan da wannan matsala ta shafa.

Ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi da muhallansu - inda dubbai suka yi kaura zuwa makwabtan kasashe - tun da ta soma kai hare-hare a 2002.

Reuters