Karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta wucin gadi, Ma'aikatar Kudin Isra'ila tana karbar haraji a madadin Falasdinawa kuma tana tura wa Hukumar Falasdinawa kudin a kowane wata. / Hoto: Reuters

Ministocin Tsaro da na Kudi sun samu sabani kan ko ya dace a tura wa Hukumomin Falasdinawa harajin da aka karba a Gabar Yammacin Kogin Jordan, lamarin da ke da alaka da tsamin dangantaka yayin da dakarun Isra'ila suka nausa da yaki cikin Gaza da kasar ta yi wa kawanya.

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya bukaci a raba kudin harajin da Isra'ila ta karba a madadin Falasdinawa a wasu bangarori na Gabar Yammacin Kogin Jordan da ke karkashin ikonta, ba tare da bata lokaci ba.

"Isra'ila tana so a samu zaman lafiya a yankunan Judea da Sumaria, a ko da yaushe musamman a wannan lokaci," in ji Gallant yayin da yake jawabi ta talabijin, inda ya yi amfani da kalmar da mutane da yawa suke amfani da ita a Isra'ila kan Gabar Yammacin Kogin Jordan, wurin da aka samu karuwar tashin hankali tun bayan fara yaki a Gaza kimanin makonni uku da suka wuce.

"Ya kamata a mayar musu da kudin ba tare da bata wani lokaci ba saboda Hukumar Falasdinawa za ta iya amfani da su wajen aikace-aikacenta da kuma bangaren hukumar da ke aikin yaki da ta'addanci," in ji shi.

"Ina ganin ya kamata a yi aiki da matsayar da majalisar ministoci ta cimma kwanakin da suka wuce," in ji shi.

A karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta wucin-gadi, ma'aikatar kudi ta Isra'ila tana karbar haraji a madadin Falasdinawa kuma tana tura wa Hukumar Falasdinawa, wacce taka da kwarya-kwaryan iko a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, amma ana ta samun ce-ce-ku-ce kan wannan tsari.

Ministan Kudi Bezalel Smotrich, wanda jam'iyyarsa mai tsattsauran ra'ayi take samun goyon baya daga wajen Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna a Gabar Yammacin Kogin Jordan, ya mayar da martani cewa Gallant ya yi "babban kuskure" bayan da ya bukaci a sakar wa Falasdinawa kudinsu.

Tun da farko Smotrich ya ce zai yi adawa da tura wa Falasdinawa kudinsu, wadanda suke amfani da su wajen biyan albashin ma'aikatan gwamnati da sauran ayyukan gwamnati, inda ya zargi Falasdinawa da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye da goyon bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

"Ba na so na bari kasar Isra'ila ta dauki nauyin makiyanmu a Judea da Sumaria wadanda suke goyon bayan ta'addancin Hamas suka kuma dauki nauyin 'yan ta'addan ranar 7 ga watan Oktoba wadanda suka yi mana kisan kiyashi," in ji shi a wata sanarwa da ya fitar.

Ba wannan ne karo na farko da ministocin biyu suke kin zama a ihu daya ba, don ko a farkon wannan shekarar lokacin da Firaiministan Benjamin Netanyahu ya sauke Gallant kan adawarsa da shirin shugaban na yi wa bangaren shari'ar kasar garanbawul, kafin daga bisani ya janye aniyyarsa bayan ya fuskanci adawa daga al'umma.

TRT World