Nijeriya ta samo tallafin dala 600,000 ga al’ummomin ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar, "musamman ma na Maiduguri," daga Gidauniyar Bill and Melinda Gates a wajen Babban Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya UNGA, da ake yi a Amurka.
Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Nijeriya kan watsa labarai Kashim Shettima Santley Nkwocha ne ya wallafa hakan a shafinsa an X a ranar Alhamis, inda ya ƙara da cewa tallafin zai kuma haɗa da inganta sauye-sauyen fannonin lafiya da na harkar noma a ƙasar.
"Musamman, Gidauniyar ta yi alkawarin bayar da dala 600,000 don magance ambaliyar ruwa a jihar Borno da sauran tsare-tsare na kiwon lafiya, tare da karin tallafin dala miliyan biyar da aka amince da su ga Makarantar Kasuwancin Legas da abokan hulda don bunkasa tattalin arzikin noma na rogo na masana'antu."
An sanar da ba da gudunmawar ne a yayin da Kashin Shettima ke ganawa da shugaban Gidauniyar Bill and Melinda Gates na duniya, Dr Christopher Elias da tawagarsa.
A yayin ganawar, Kashim Shettima ya jaddada aniyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bunƙasa harkar noma da fannin lafiya da samar da abinci mai gina jiki a gaba-gaba cikin muradunta.
Mataimakin Shugaban Kasar ya ce, "Mun himmatu matuka wajen tunkarar kalubalen ci gaban da al'ummarmu ke fuskanta musamman matsalar karancin abinci mai gina jiki."
Ya jaddada sadaukarwar gwamnatin Nijeriya wajen tabbatar da gaskiya da jagoranci mai inganci wajen tinkarar wadannan matsaloli, inda ya nuna cewa akwai bukatar gaggawa wajen samar da wuraren noman masara a karkashin shirin Telemaze.
Da yake yin alƙawarin daukar matakin gaggawa kan ba da izinin shigo da tsaba na ƙwararrun iri, VP ya ce, "Mun fahimci mahimmancin mahimmancin samar da abinci da bunƙasa aikin gona na masana'antu. Shirin haɓaka rogo, musamman, yana da babbar dama ga tattalin arzikinmu.