An ga hayaki na tashi a lokacin da aka kai hari ta sama a Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye. Hoto/ Raneen Sawafta/Reuters

Dakarun Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla uku, ciki har da karamin yaro, da kuma raunata akalla mutum 29 a harin da suka kai a titunan birnin Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana.

“Mutum uku sun rasu, 28 sun samu raunuka sakamakon harin da Isra’ila ta kai birnin Jenin,” kamar yadda sanarwar ma’aikatar ta bayyana a ranar Litinin.

Ta bayyana cewa Khaled Asasa, mai shekara 21, da Qassam Abu Sariya, mai shekara 29, da Ahmed Saqr, mai shekara 15, na daga cikin wadanda aka kashe.

Mataimakin gwamnan Jenin, Kamal Abu al-Rub, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa dakarun Isra’ila sun kaddamar da harin da misalin karfe 4:00 na asuba agogon kasar (0100 GMT).

“Sojoji da dama sun far wa sansanin ‘yan gudun hijirar Jenin da kuma birnin bayan sallar asuba, kuma an yi musayar wuta mai karfi,” in ji shi.

Wani mai daukar hoto na AFP da ke Jenin ya tabbatar da cewa ana ci gaba da musayar wuta har zuwa 8:40 na safe (0540 GMT). Wannan rikicin shi ne na baya-baya a sama da shekara guda da aka kwashe ana fafatawa kusan kullum tsakanin Isra’ila da Falasadiniwa ta Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Sojojin Isra’ila ba su fito nan take sun yi magana kan wannan lamari ba. Sai dai kafafen watsa labarai na Isra’ila sun rawaito cewa an raunata dakarunsu da dama a rikicin.

Wani bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba daga Jenin ya nuna yadda wani jirgi na Isra’ila ya harba makamin roka a yayin da ake luguden wuta.

Isra’ila da Falasdinawa sun shafe watanni suna rikici wanda ya fi kamari a Gabar Yamma da Kogin Jordan inda aka kashe Falasdinawa 120 a bana.

Isra’ila na yawan kai samame da daddare a yankin da ta mamaye tare da cewa akasarin wadanda ke mutuwa “mayaka ne” sai dai matasan da ke jifa da duwatsu da wasu da ba su saka kansu a rikicin ba su ma an kashe su.

A martanin da ta mayar, hare-haren da Falasdinawa suka kai kan ‘yan Isra’ila ya yi sanadin mutuwar akalla 'yan Isra’ila 20 a bana.

TRT World