Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya ta dakatar da jiragen da ke jigilar Kiristocin da ke zuwa aikin ibada Isra’ila saboda yadda rikici tsakanin mayaƙan Hamas da Isra’ilan ke ta’azzara.
Shugabar hukumar tsara zuwa ibada ta Kiristoci ta Nijeriya NCPC, Florence Gbafe, a wata sanarwa ta ce an dakatar da tashin jiragen rukuni na biyu na masu ibadar da aka tsara tun da fari zai tashi ranar Talata, kamar yadda Reuters ya rawaito.
“Ga dukkan wadanda suke cikin rukuni na biyu na zuwa ibada Isra’ila, muna sanar da ku cewa a yanzu an dakatar da tafiya ibadar saboda halin da ake ciki a Isra’ila.
“Za mu sanar da ku duk wani bayani nan gaba idan ya taso,” ta ƙara da cewa.
Ta ce gwamnatin Nijeriya da Jihar Legas za su ci gaba da ba da muhimmanci kan kare rayukan ƴan ƙasar da kuma hana su shiga duk wata matsala a wajen Nijeriya.
Gbafe ta ce NCPC da Jihar Legos, za su sanya wata ranar ta jigilar sauran maniyyatan.
Fiye da ƴan Nijeriya 340 da suke gudanar da ibadar Kiristoci ta tsakiyar shekara a Isra’ila suka samu damar shiga ƙasar Jordan da ke maƙwabtaka da Isra’ila don ziyartar sauran tsarkakan wuraren da ke can, a lokacin da rikici ya ɓarke a Isra’ila da Falasɗinu, kamar yadda hukumar NCPC ta faɗa a ranar Litinin a wajen yi wa maniyyatan bita.
Fiye da Kiristoci 10,000 ne suke zuwa Isra’ila da Falasɗinu duk shekara don gudanar da aikin ibada.