Ba zan iya lissafa yawan mutanen da ke kawo mana ƙorafin cewa ana tatsarsu kuɗaɗe ta hanyar yi musu barazanar yada hotunan tsiraicinsu ba. Hoto: Benjamin Hundeyin

Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas a kudu maso yammacin Nijeriya ta gargadi masu tura wa mutane hotunan tsiraicinsu da su guji yin hakan don samar wa kansu kwanciyar hankali da kare mutunci.

A wani gajeren saƙo da mai magana da yawun rundunar, SP Bejamin Hundeyin ya wallafa a shafin X, ya ce yana wannan gargaɗi ne saboda irin yawan masu kai ƙorafin cewa ana ƙoƙarin ɓata musu suna ta hanyar yaɗa hotuna ko bidiyon tsiraicinsu da suka taɓa aika wa wasu.

Ana yawan samun lamarin da hotuna ko bidiyo na tsiraicin mutane ke yaduwa a intanet, abun da ke ɓata musu suna da taɓa darajarsu a idon al’umma, ko kuma a dinga amfani da hakan wajen tatsar mutane kuɗaɗe da nufin ko su bayar ko a yaɗa su.

“Ba zan iya lissafa yawan waɗanda, ciki har da manyan mutane da ke kawo mana ƙorafin cewa ana tatsarsu kuɗaɗe ta hanyar yi musu barazanar yada hotunan tsiraicinsu ga al'umma ba,” in ji SP Hundeyin.

Hundeyin ya ƙara da cewa “idan har ya zama wajibi ka aika hotunan tsiraicinka to ka sanya shi a tsarin da sau ɗaya wanda ka aikawa zai iya kalla ko kuma ka rufe fuskar da wata alama”.

Ya kuma ce ka da a manta cewa ko da kiran bidiyo mutum ya yi to ana iya daukar hotonsa a haka ko a nada a yi amfani da shi wajen ɓata masa suna.

“Duk da cewa dai wasun ana ɗaukarsu a bidiyon ne ba tare da sun sani ba, inda ake nadar lokacin da suke cikin shauƙi ba tare da izininsu ba,” ya ce.

“Kar ka amince da kowa. Ku ɗauki matakan hana faruwar hakan. Ku yi taka tsantsan.”

Jami’in ƴan sandan ya bayar da adireshin shafin intanet na ƴan sanda da ya ce mutane za su iya amfani da shi wajen shigar da ƙorafi idan har suka samu kansu a irin wannan siratsi.

TRT Afrika