Hukumomin biyu sun shafe wajen shekara 20 suna aiki a haraba daya a ofisoshinsu da ke Ikoyi a Legas/ Hoto: Twitter

Sa’insa ta barke tsakanin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati EFCC da hukumar tsaro ta farin kaya DSS na Nijeriya a ranar Talata, kan batun yi wa ofishin EFCC kawanya da suka zargi DSS da yi.

Tun da farko hukumar EFCC ce ta wallafa sako a shafinta na Facebook cewa jami’an DSS sun yi wa ofishinta da ke kan Titin Awolowo a unguwar Ikoyi da ke Jihar Legas kawanya a safiyar Talatar, 30 ga watan Mayun 2023, inda suka hana ma’aikatan wajen shiga.

“Jami’an DSS sun yi wa ofishin EFCC kawanya da motoci masu silke. Wannan lamari ya zo da matukar mamaki ga hukumar ganin cewa mun shafe shekara 20 muna tare a haraba daya da hukumar DSS ba tare da samun wata matsala ba,” in ji sanarwar.

DSS’ Siege on Our Lagos Office Shocking - EFCC The operatives of the Lagos Command of the Economic and Financial Crimes...

Posted by Economic and Financial Crimes Commission on Tuesday, May 30, 2023

Sai dai tuni ita ma hukumar DSS ta wallafa martani kan batun a shafinta na Twitter tana mai karyata rahotannin da ta ce ta samu na cewa ta yi wa ofishin EFCC kawanya tare da hana ma’aikatan hukumar shiga.

“Wannan ba gaskiya ba ne. Hukumar ta yi kawanya ne kawai wa yankin da yake karkashin ikonta inda take gudanar da ayyukanta nay au da kullum.

Karin bayanin EFCC

Hukumar EFCC wacce ta ce ta kadu kwarai da abin da ya farun, ta ce hana jami’anta shiga ofis na nufin kawo tsaiko ga ayyukan hukumar a ofishinta mafi girma da ke da ma’aikata fiye da 500.

“Sannan kawanyar za ta jawo tsaiko ga ayyukan da ake yi a kan daruruwan bayanai da masu laifin da ake tsare da su.

“Matsalolin da aka yi niyyar kai su kotu yau don saurarar kararraki duk an kawo musu tsaiko, yayin da mutanen da aka gayyata a don gabatar da tuhuma a kansu duk an bar su ba tare da yin hakan ba,” in ji sanarwar EFCC.

EFCC ta kara korafin cewa “wani babban abin daga hankalin ma shi ne yadda aka bar masu laifin da ke tsare a cikin ofishin babu wata kulawa inda hakan zai zama take hakkokinsu a matsayin su na fursunoni.

“Dukkan wadannan za su yi mummunan tasiri a kan yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati da ake yi."

EFCC ta kuma ce abin da DSS din ta yi ya yi karo da hadin kan da ake sa ran hukumomin biyu da ke yi wa kasar aikin su yi, musamman a lokacin da ake tattaunawa kan wani muhimmin batu.

Karin bayanin DSS

A sanarwarta mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta Peter Afunanya, DSS ta ce “babu wani ce-ce-ku-ce da ya faru a ofishi mai lamba 15A kan Titin Awolowo kamar yadda kafafen watsa labarai suka fada.

“Shin EFCC ta ce muku ana gasa ne kan hakkin mallakar ginin? Zan yi mamaki idan tana gasa ne kan hakkin mallakarsa.

“Ofishin Titin Awolowo shi ne hedikwatar hukumar tsaro ta farin kaya tun ta da can wato NSO. A can DSS ta fara. Abu ne da kowa ya sani. Abu ne da yake a tarihi. Ku je ku bincika.

“Babu wata gaba tsakanin DSS da EFCC a kan ko ma me ye. Don Allah kar ku kirkiro wata gaba. Manyan abokan huldarmu ne su da muke aiki tare don inganta kasar nan. Ku yi watsi da duk wata karya," sanarwar ta karkare da fada.

TRT Afrika da abokan hulda