Shugaban Gwamnatin hadin-kan kasa ta Libya Abdul Hamid Dbeibah ya dakatar da Ministar Harkokin Wajen kasar Najla Mangoush sannan ya bukaci a gudanar da bincike a kanta, a cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.
An dauki matakin ne a yayin da a ranar Lahadi Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Eli Cohen ya ce ya gana da takwararsa ta Libya a karon farko a tarihin kasashen biyu.
A wata sanarwa da Ma'aikatar Wajen Isra'ila ta fitar, Cohen ya bayyana ganawar da ya yi da Najla Elmangoush a birnin Rome a makon jiya a matsayin mai "cike da tarihi".
Babban jami'in diflomasiyyar na Isra'ila ya kara da cewar ganawar tasu ita ce “matakin farko na kyautata dangantaka tsakanin Isra'ila da Libya.”
"Girma da kuma matsayin Libya sun sa tana da matukar muhimmanci ga kasar Isra'ila," in ji Cohen.
Ministan Harkokin Wajen Italya Antonio Taiani ne ya shirya ganawar ta farko tsakanin ministocin harkokin wajen Isra'ila da Libya.
Kawo yanzu gwamnatin Libya ba ta ce komai ba game da kalaman Ministan Harkokin Wajen na Isra'ila ba.