Wani jirgin ruwan rundunar soji ta China's People's Liberation Army (PLA) mai suna Nanning ya isa Najeriya ranar Lahadi a wata ziyara ta ba kasafai ba.
Ana kallon wannan mataki a matsayin wani muhimmin yunkuri na Beijing na kyautata dangantaka da tasirinta a Afirka.
Jakadan China a Najeriya ya bayyana wannan ziyara ta kwanaki biyar a matsayin wani babban al'amari game da huldar dangantaka, yayin da rundunar sojin ruwan Nijeriya ta ce a shirye take ta yi aiki da China wajen magance rashin tsaron da ake fuskanta a Gabar tekun Guinea, a cewar wata sanarwa da ofishin jakadancin China ya fitar ranar Litinin.
Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta fitar da sanarwar da ke cewa jirgin ruwan Nanning, wanda ya samu rakiyar wani karain jirgi mai suna Sanya, tare da jirgin Weishanhu, sun isa gabar tekun Lagos ranar Alhamis.
Dangantaka ta kut-da-kut da kasashen Afirka
Nijeriya na cikin kasashen da suka fi fitar da man fetur zuwa kasashen waje. Angola da Nijeriya na cikin kasashen Afirka da suka fi sayar wa China fetur. Kazalika babban kamfanin hakar mai na China CNOOC Ltd yana aikin hakar mai a gabar tekun Nijeriya.
A watan Janairu, Nijeriya ta bude tashar jiragen ruwa ta biliyoyin dala da China ta gina a Lagos. Kamfanin China Harbour Engineering Co da kamfanin Tolaram da ke Singapore ne suka mallaki kashi 75 cikin dari na sabuwar tashar da ke Lekki.
Haka kuma ana rade-radin cewa China za ta kai sojojinta Gabar Tekun Guinea. A bara, jami'an tsaron Amurka sun bayyana fargabarsu cewa yin sansanin China a yankin, watakila a Equatorial Guinea, zai zama barazana ga Amurka.