Wani abin da ya ja hankali wajen bikin sanya-hannu kan sabon kundin tsarin mulkinn kasar, shi ne yadda shugaban Mali Assimi Goita ya bayyana a gaban teburin da aka ajiye karamin samfurin jirgi mara matuki na Bayraktar AKINCI, kirar Turkiyya ./Hoto: AA

Sabon kundin tsarin mulkin Mali ya jefar da Faransanci a matsayin harshen da ake mu'amala da shi a hukumance a kasar tun shekarar 1960.

Kuri'ar raba-gardama da aka kada wadda ta samar da sabon kundin tsarin mulkin na Mali, wacce kashi 96.91 na 'yan kasar suka amince da ita ranar 18 ga watan Yuni, ta yi watsi da Faransanci a matsayin harshen da ake hulda da shi a hukumance.

Daga yanzu harsunan-uwa guda 13 na kasar ta Mali za su kasance wadanda ake hulda da su a hukumance, sannan Faransanci zai zama harshen da za a rika mu'amala da shi a wurin aiki kawai.

'Yan kasar Mali suna magana da harsuna kusan 70 kuma wasu daga cikinsu, da suka hada da Bambara, Bobo, Dogon da Minianka, an ba su matsayi na harsunan kasa a karkashin dokar soji ta 1982.

Ranar Asabar, shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali Kanar Assimi Goita ya sa an soma amfani da sabon kundin tsarin mulkin, abin da ke nuna cewa an shiga Jamhuriya ta Hudu a kasar, a cewar fadar shugaban kasa.

Tun bayan da suka kwace mulki a watan Agustan 2020, sojojin Mali sun bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasar zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wurin sake gina kasar.

Sau biyu ana yin juyin mulki a Mali a baya-bayan nan, a Agustan 2020 da kuma a watan Mayun 2021.

Tun da fari gwamnatin sojin kasar ta yi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabrairun 2022 amma daga bisani ta dage shi zuwa Fabrairun 2024.

Jirgin yakin Bayraktar Akıncı na Turkiyya

Wani abin da ya ja hankali wajen bikin sanya-hannu kan sabon kundin tsarin mulkinn kasar, shi ne yadda shugaban Mali Assimi Goita ya bayyana a gaban teburin da aka ajiye karamin samfurin jirgi mara matuki na Bayraktar AKINCI, kirar Turkiyya.

Ana kiran tsohon tsarin mulkin kasar Mali da tsarin mulkin zamanin mulkin-mallaka, kuma hakan ya kara nuna muhimmancin kwaskwarimar da aka yi wa tsarin mulkin kasar.

Dakarun sojin Turkiyya sun fara amfani da bangarori uku na farko na jirgin yakin a ranar 29 ga watan Agustan 2021. Jirage marasa matukan na iya aiwatar da ayyukan da ake yi da manyan jiragen yaki.

Bayraktar Akıncı yana amfani da wani tsaron lantarki, da tsarin sadarwa na tauraron dan azam da wani tsari na "yin layar zana".

AA