Shugaban kasar Iran ya fara wata ziyara da ba kasafai yake yin irin ta ba zuwa nahiyar Afirka, a yayin da kasarsa, wacce ke cikin takunkuman tattalin arziki na Amurka, ke neman karfafa dangantakar diflomasiyya a fadin duniya.
Ziyarar da Shugaba Ebrahim Raisi ya kai Kenya a ranar Laraba ita ce ta farko zuwa nahiyar Afirka da wani shugaban kasar Iran ya taba kai wa a cikin fiye da shekara 10.
Ana kuma sa ran zai ziyarci Uganda da Zimbabwe inda zai gana da shugabannin kasashen.
Afirka "nahiya ce mai tattare da damarmaki" kuma babban waje ne da ke dauke da kayayyakin Iran, kamar yadda Raisi ya shaida wa 'yan jarida.
Sai dai bai amsa tambaya ko daya ba daga manema labarai. "Dukkanmu babu wanda ya gamsu da yawan kasuwancin da ke tafiya tsakaninmu," ya ce.
Shugaban na Iran musamman ya ambaci ma'adanan da Afirka ke da su da kuma ilimin Iran na sarrafa sinadaran fetur, amma daga cikin wadannan batutuwan babu wanda ya fito a cikin yarjejeniya biyar din da aka cimma tsakanin Iran da Kenya a ranar Laraba.
A maimakon haka, sun tabo batutuwan da suka shafi watsa labarai ne da sadarwa da fasaha da kasuwancin kifi da lafiyar dabbobi da samar da su da kuma bunkasa zuba jari.
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce Iran "babbar kawa ce mai muhimmanci a tsare-tsare" kuma "gagaruma ce wajen kirkire-kirkire a duniya".
Ya bayyana sha'awarsa ta fadada fitar da kayayyakin amfanin gona na Kenya zuwa Iran da yankin Tsakiyar Asiya fiye da ganyen shayi da ake fitarwa.
Iran tana kuma da niyyar kafa masana'antar motoci a birnin Mombasa da ke da tashar jiragen ruwa a Kenya, kamar yadda Shugaba Ruto ya ce.
Shugaba Raisi na ziyara a Afirka ne don "karfafa dangantakar tattalin arziki da ta siyasa da kasashen da yake kawance da su, tare da ganin kasarsa tana fitar da kaya zuwa Afirka," kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Iran ta fada a wata sanarwa.
Karfafa dangantakar diflomasiyya
A watan da ya gabata, shugaban kasar Iran ya kai ziyararsa ta farko zuwa yankin Latin Amurka, inda ya je Venezuela da Cuba da kuma Nicaragua.
A watan Maris kuwa, Iran da Saudiyya suka amince da farfado da alakar diflomasiyyarsu a wani lamari na tarihi.
Iran tana ta kai ruwa rana da Kasashen Yamma a kan shirinta nukiliya, wanda ya kai wata gaba cikin shekara biyar da suka wuce, tun bayan da Shugaba Donald Trump ya janye yarjejeniyar da ta hana shirin wanzuwa. Trump ya kuma sake sanya takunkumai kan Iran wadanda suka jawo matsin tattalin arziki sosai.
A watan da ya gabata Amurka ta zargi Iran da samar wa Rasha wasu kayayyaki da za ta gina kamfanin kera jirage marasa matuka, a yayin da Rasha ke neman makamai a ci gaba da yakin da take yi a Ukraine.
Iran ta ce ta samar da jirage marasa matuka ga Rasha kafin fara yakin amma tun bayan nan ba ta sake ba ta ba.
Kenya ce cibiyar kasuwanci ta Gabashin Afirka kuma kawa ce ga Amurka, inda har matar Shugaba Joe Biden, Jill ta ziyarci kasar a farkon shekarar nan.
A bara kuma, Amurka da Kenya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a kan "hadin kai kan tsare-tsaren nukiliya. Kenya ta bayyana sha'awarta ta amfani da nukiliya don samar da wutar lantarki.