Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin inganta huldar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da kasashen duniya./Hoto: Shafin Facebook na Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya umarci dukkan jakadun kasar daga ko'ina a kasashen duniya su koma gida nan-take.

Ya bayyana haka ne ranar Asabar a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar.

"Shugaban kasa ya ba da umarnin ne bayan ya yi nazari a tsanake game da halin da manya da kuma kananan ofisoshin jakadancin Nijeriya ke ciki a fadin duniya, da kuma shirin shugaban kasa na sabunta al'amura," in ji sanarwar.

Kakakin shugaban kasar ya ce Shugaba Tinubu ya sha alwashin inganta huldar jakadancin kasar da kasashen waje ta yadda za ta dace da zamani da kuma biyan bukatun 'yan kasar.

"A kan haka ne Shugaban kasar ya bayar da karin umarni a cire wakilin Nijeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York da kuma Geneva daga cikin wadanda za su dawo gida" saboda babban taron majalisar da za a yi nan gaba a wannan wata.

TRT Afrika