Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas a Kudancin Nijeriya ya ziyarci al’ummar Hausawa mazauna yankin Agege don rarrashin su kan zargin cin zarafin da wasu jami’an ‘yan sanda suka yi wa wani dan acaba a kwanakin baya.
Kwamishina Idowu Owohunwa ya kai ziyarar ne a ranar Alhamis sakamakon bazuwar wani bidiyo da ke nuna yadda wasu jam’ian ‘yan sanda "suka yi amfani da karfi fiye da kima a kan dan acaban. "
Yaduwar bidiyon wanda aka fara wallafa shi a shafukan sada zumunta ranar 12 ga watan Mayun nan, ya harzuka ‘yan kasar da dama inda aka dinga yin Allah-wadai da ‘yan sandan.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar reshen Jihar Legas SP Benjamin Hundeyin ya wallafa a Twitter ta ce “Kwamishinan ya yi tur da amfani da karfi da ‘yan sandan suka yi wajen tursasa wa dan acabar bin dokar haramta amfani da babur da take aiki a wasu sassan jihar.”
Sanarwar ta kuma ce Mista Idowu ya tabbatar wa al’umma cewar za a sanar musu irin matakin da aka dauka na ladabtar da jami’an da zarar an yi hakan.
Me ya faru a bidiyon?
An fara sakin bidiyon mai tsawon dakika 45 ne a shafukan sada zumunta ranar 12 ga watan Mayun nan.
Masu wallafa bidiyon sun ce lamarin ya faru ne a ranar, a Oja Oba, titin Ogundele street, kusa da karkashin gada a Abule Egba.
An ga dan acabar a kwance a kasa da babur dinsa a yashe a gefe, sai kuma ‘yan sanda uku da ke tsaye a kansa suna umartarsa da ya tashi.
Daga baya suka daga shi, yayin da daya daga cikin jami’an ya hau babur din yana tukawa, lamarin da ya sa dan acabar ya zabura don karbar abinsa.
Sai dai sauran ‘yan sandan biyu sun yi wuf sun hana shi hakan, inda daya daga cikinsu ya doke shi da wata babbar gora da ke hannunsa.
A karshe dai dan sanda ya samu nasarar wucewa da babur din, su kuma sauran biyun suka shiga babur mai kafa uku na Keke Napep ya tafi da su.
An jiyo wasu mutane wadanda ga dukkan alamu su suke nadar bidiyon suna umartar mai babur din da ya bi su, daga baya kuma sai aka ji su nace masa ya dawo.
Bayan hakan ne sai aka hasko fuskar mai babur din jini yana ta kwarara daga goshinsa da ya dafe da hannu.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce rundunar za ta ci gaba da tabbatar da cewa an bi doka da oda a kasar.
Yabo da jinjina
Masu sharhi a shafukan sada zumunta sun yi ta yabon rundunar ‘yan sandan kan yadda ta yi gaggawar daukar mataki kan lamarin.
Wani mai suna Afolabi ya ce: "A hankali dai ana samun sauyi a Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya har suna zuwa su gana da wanda aka zalinta? Allah Ya yi wa Baba Alkali albarka.
Wani mai suna Introvert shi kuma cewa ya yi: "Soshiyal midiya ta sake yin nasara bayan kwana biyar kacal. Hakan ya yi kyau."
Mun gode wa Allah da samun soshiyal midiya! Ba wani abu da zai sake boyuwa na rashin iya aikin 'yan sanda. Ta hakan ne kawai za a samu sauyi."