Wike ya ce Abuja na fuskantar matsalolin tsaro kamar sauran birane na duniya. Hoto/FCTA

Hukumar Kula da Birnin Tarayyar Abuja a Nijeriya ta sanar da cewa za ta kulla alaka da kasar Isra’ila domin samar da tsaro da tallafa wa matasa da kuma samar da ayyukan yi.

Ministan Abuja Nyesom Wike ne ya bayyana haka a ranar Talata bayan ya karbi bakuncin jakadan Isra’ila a Nijeriya Mista Michael Freeman.

Ministan ya shaida wa jakadan na Isra’ila cewa Abuja na da yanayi mai kyau wanda za a iya noma kuma akwai shiri da gwamnati take da shi a kasa domin kafa manyan gonaki wadanda matasan Nijeriya za su samu ayyukan yi.

A bangaren tsaro kuwa, Mista Wike ya bayyana cewa Abuja kamar sauran birane na duniya na fuskantar kalubale na tsaro inda ya ce kofa a bude take domin su hada hannu da Isra’ila don inganta tsaro a Abuja.

Wannan tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar rashin tsaro a Abuja musamman matsalolin garkuwa da mutane.

Ko a cikin watan nan na Satumba sai da aka sace mutum 19 a Karamar Hukumar Bwari da ke birnin tarayyar.

Haka kuma ‘yan sanda a Abuja sun sanar da kama masu garkuwa da mutane 11 a fadin birnin.

Tun bayan da Mista Wike ya samu mukamin Ministan Abuja, ya aiwatar da sauye-sauye da dama a birnin daga ciki har da sallamar shugabannin hukumomi 21 na birnin.

TRT Afrika