Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kashe shugabannin 'yan bindiga da dama da ɗaruruwan mayaƙa a ƙasar bayan sabbin hare-hare da aka kai a watanni uku na wannan shekarar.
Kakakin rundunar sojin Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Nijeriya na fama da rashin tsaro a faɗin ƙasar ciki har da na ƙungiyar ta'adda mai iƙirarin kare Musulunci da ke da shekaru 15 a arewa maso-gabas, rikicin 'yan a-ware a kudu maso-gabas, yawaitar satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta da garkuwa da mutane don neman fansa a arewa maso-yammacin ƙasar.
Kakakin Rundunar sojin Manjo Janar Buba ya ce "Farmakin da dakarunmu suka kai sun yi sanadiyar kashe manyan shugabannin 'yan ta'adda 65."
"A watanni uku na wannan shekarar, dakarunmu sun kawar da 'yan ta'adda 1,937, sun kama 'yan ta'adda 2,782 da kuma wasu masu aikata manyan laifuka tare da kuɓutar da mutane 1,854 da aka yi garkuwa da su," in ji Buba a sanarwar da ya fitar.
'Yan bindigar da sojojin suka kashe sun haɗa da 'yan ta'addar Boko Haram, mayaƙan Daular Musulunci ta Yammacin Afirka, da ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da dama. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Halilu Sububu, wanda sojoji suka taɓa bayyana cewa suna neman sa ruwa-a-jallo a 2022 tare da saka diyyar naira miliyan biyar ga duk wanda ya faɗi inda yake.
A farkon watan Satumba, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarni ga Ministan Tsaro da manyan kwamandojojin soji da su koma jihar Sokoto da ke arewa maso-yamma, ɗaya daga jihohin da ta'addanci ya yi ƙamari, domin su yaƙi ta'addanci.
Tun wancan lokaci, sojojin sun ƙarfafa kai farmaki da samame kan 'yan bindiga ta sama da ta ƙasa.