1240 GMT –– Wani hari da Isra'ila ta kai kan wani gini a Beirut ya kashe jami'in yaɗa labarai na kungiyar Hezbollah Mohammad Afif, kamar yadda wasu majiyoyin tsaron kasar Lebanon suka sanar, ko da yake babu wani tabbaci daga Hezbollah.
An kai harin ne a unguwar Ras al-Nabaa wanda unguwar ta kasance wani wuri wanda mutane da dama waɗanda suka rasa matsugunansu daga yankunan kudancin birnin Beirut sakamakon hare-haren Isra’ila ke neman mafaka.
Majiyar tsaron ta ce Isra’ila ta kai harin ne kan wani gini da ofisoshin jam'iyyar Ba'ath suke, kuma shugaban jam'iyyar ta ƙasa Ali Hijazi ya shaida wa kafar yada labaran kasar ta Al-Jadeed cewa Afif na cikin ginin.
1125 GMT –– Akalla Falasdinawa 96 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka jikkata sakamakon hare-haren da jiragen yakin Isra'ila suka kai arewaci da tsakiyar Zirin Gaza a ranar Lahadi, a cewar hukumomin yankin.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan wasu gine-gine da gidaje a arewacin birnin Beit Lahia da kuma sansanonin 'yan gudun hijira na Nuseirat da Bureij a tsakiyar Gaza.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce sama da mutane 72 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a Beit Lahia, yayin da wasu Falasdinawa 24 suka mutu, wasu 60 kuma suka jikkata a tsakiyar Gaza.