Babban Bankin Ghana ya ce a makon da ya gabata zai dauki lokaci mai tsawo kafin hauhawar farashin kaya ya dawo tsakanin kashi 6 zuwa 10 cikin 100. / Hoto: Reuters

Hauhawar farashi a Ghana ta ragu zuwa kashi 23.5 cikin 100 daga kashi 23.8 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta Ghana GSS ta tabbatar a ranar Litinin.

Farashin kayayyakin abinci a watan Janairun na kan 252.6 idan aka kwatanta da 204.5 a Janairun 2024.

Haka kuma hukumar ta GSS ta bayyana cewa hauhawar farashi na wata-wata tsakanin Disamban 2024 zuwa Janairun 2025 na kan kashi 1.7 cikin 100.

Hauhawar farashin kayayyakin abinci ya kasance abu mai muhimmanci inda ya kai 28.3 a watan Janairu, wanda hakan ke nufin an samu ƙaruwa da 2.06.

Haka kuma hauhawar farashin da ba ta kayan abinci ba ta kasance a kan kashi 20.3 wanda hakan ya nuna an samu madaidaiciyar ƙaruwa da kaso 1.4 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Hauhawar farashi a kan kayayyakin da aka samar a cikin ƙasa na kan kashi 25.7 a Janairu, inda kuma hauhawar farashi ga kayayyakin da aka shigar da su ƙasar ya tsaya a kan kashi 18.4.

Kasar da ke yammacin Afirka na farfaɗowa ne daga matsalar tattalin arziki mafi muni a tsawon lokaci, tare da tashe-tashen hankula a masana'antun koko da na zinare.

Duk da haka, hauhawar farashin ƙasar ya kasance fiye da kashi 8 na Bankin Ghana tare da tazarar maki 2 cikin 100 na kowane bangare.

Babban bankin ya ce a makon da ya gabata zai dauki lokaci mai tsawo kafin hauhawar farashin kaya ya dawo tsakanin kashi 6 zuwa 10 cikin 100.

TRT Afrika da abokan hulda