Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana faruwar gobarar a matsayin abin takaici matuka.

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Nijeriya sun ce an yi jana'izar almajirai 17 a ranar Laraba, wadanda suka mutu a wata mummunar gobara da ta tashi a makarantar allonsu a jihar.

Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne da tsakar daren Talata a makarantar allon da ke ƙaramar hukumar Kaura-Namoda bayan da ta shafe kusan awa uku tana ci.

Lamarin ya kuma jikkata wasu almajiran 16.

Wani mazaunin yankin Abdulrasaq Bello Kaura ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa wutar ta tashi ne a wajen da ake jibge karare.

"Abin ya faru ne a ɗakin kwanan almajirai da ke Makarantar Allon Mallam Ghali. Wajen almajirai 100 ke kwana a wajen, bayan kwashe su daga wajen bisa tsammanin babu wanda ya saura, sai daga baya aka ga ƙafafu da hannayen wasu almajiran da wutar ta ƙone su ƙurmus," in ji shi.

Ya ce tuni aka yi jana'izar almajiran 17 a ranar Laraba.

Gwamnatin Zamfara ta jajanta

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana faruwar gobarar a matsayin abin takaici matuka.

A wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya ambato gwamnan na cewa “Na ji takaicin gobarar da ta tashi a ranar Talata a Makarantar Mallam Ghali, makarantar Almajirai da ke karamar hukumar Kauran Namoda.

“A madadin gwamnatin jihar Zamfara, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai da makaranta, da sauran al’umma baki daya yayin da muke jimamin rashin wadannan ɗalibai.

“A cikin wannan lokaci na bakin ciki, Allah Ta’ala ya ba mu hakuri da juriya, kuma muna miƙa ta’aziyya ga iyalan da ke cikin bakin ciki yayin da suke cikin wannan mawuyacin lokaci.

"Ina mika fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. “A matsayinmu na gwamnati da alhaki ya rataya a wuyanmu, za mu binciki musabbabin faruwar wannan gobara tare da lalubo hanyoyin da za mu hana afkuwar ta a nan gaba.

"Za mu ba da duk wani tallafi da taimako ga iyalan wadanda abin ya shafa."

TRT Afrika