Tsohon gwamna Matawalle bai yi nasarar cin zabe karo na biyu ba. Hoto. /  Facebook: Bello Mohammed Matawalle

Takaddama ta barke tsakanin jami'an tsaro da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, bayan da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DDS, suka kai samame gidansa a ranar Juma'a.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun kwace wasu motoci a cikin gidan Matawallen da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Hakan na faruwa ne kwanaki bayan sabon gwamnan jihar Dauda Lawal ya yi zargin cewa Matawalle ya kwashe wasu motocin alfarma da gwamnantin jihar ta saya daga gidan gwamnati.

A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar APC reshen Jihar Zamfaran ta yiAllah-wadai da abin da ta kira "kutse da lalata kayayyaki da 'yan sanda dajami'an hukumar tsaro ta farin kaya DSS suka yi a gidan tsohon gwamnan."

"Wannan kutse ya taka dokar sashe na 34 da 35 da 37 da 41 da 42 da kuma 43 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999," in ji sanarwar.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun kwashe motoci hudu daga gidan tsohon gwamnan suka tafi da su. Sai dai har zuwa wannan lokacin, rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara ba ta ce komai kan batun.

Amma a sanarwar jam'iyyar APC mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na reshen jihar, Yusuf Idris Gusau, ta kara da cewa ba su san dalilin da ya sa aka kai samamen ba.

Jam'iyyar APC ta kuma yi kira ga hukumomin 'yan sanda da DSS da su dauki mataki kan wadanda suka aikata hakan.

Sai dai har zuwa yanzu ba a ji ta bakin Gwamna Dauda Lawal ba kan wannan abu da ya faru na kai samamen.

Amma da ma tun bayan rantsar da shi an ambato shi yana zargin Matawalle da tafiya da motocin gwamnati da dama, da ma wasu kayayyakin cikin gidan gwamnatin kamar talabijin da kuka gas.

"Idan gwamnati na tunanin cewa tana da wata matsala da tsohon gwamna,me ya sa ba za ta kai shi kotu ba, maimakon yin wannan abin da ya takadoka", in ji sanarwar APC.

TRT Afrika