Daga Abdulwasiu Hassan
Nasarar da wasu 'yan siyasa suka samu a zaben gwamnoni na jihohin Nijeriya ta ja hankalin jama’a kuma hakan zai sa a zuba ido sosai don ganin kamun ludayinsu a shekaru hudu da ke tafe.
Irin yadda wadannan sabbin gwamnonin suka yi gwagwarmaya da 'yan hamayya har suka kai ga yin nasara a zabukan watan Maris na 2023 na cikin dalilan da suka sa salonsu na gudanar da mulkin jihohinsu zai ja hankalin jama’a a ciki da wajen jihohin.
Wasu daga cikinsu sun kayar da gwamnoni da ke kan mulki, wasu kuwa sun yi ba-zata ne.
Ga wasu daga cikinsu:
Me Abba Gida-Gida zai yi a Kano?
Kano Jalla Babbar Hausa! Kamar yadda kirarin nata yake, haka ma salon siyasarta ke daukar hankali. Shi ya sa ma akan ce, "Siyasar Kano, Sai Kano!"
A 2023 ma zaben gwamna na Jihar Kano na daga cikin wadanda aka fi tattaunawa a kansu a fadin kasar, musamman ganin yadda daya daga cikin fitattun 'yan takarar ya tsaya a karkashin sabuwar jam'iyya ta NNPP.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta ayyana Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani Abba Gida-Gida, na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, bayan samun kuri’a 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC mai mulki ya samu kuri’a 890,705.
Abba ya taba zama Kwamishinan Ayyuka a lokacin da jagoran jam’iyyarsa ta NNPP Rabiu Musa Kwankwanso ke gwamnan jihar Kano, kuma ya shafe sama da shekara 30 yana aiki da Kwankwaso.
Shi kuma Nasiru Gawuna shi ne mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado.
Wannan ya sa ana ganin zaben da Abba ya ci ya kasance tamkar zabe ne tsakanin Kwankwaso da Ganduje, kuma hamayya ta yi kamari sosai a lokacin zaben inda magoya bayan bangarorin biyu suka yi iya kokarinsu don samun nasara.
Duk da cewar jam’iyyar APC ta shigar da kara a kotu don kin yarda da sakamakon zaben, mutane sun zura ido domin ganin salon kamun ludayin Abba Kabir Yusuf a mulkin jihar Kano.
Rahotanni sun ce yawancin ayyukan raya kasa da gwamnatin Kwankwaso ta yi, a lokacin da Abba Kabir Yusuf yake Kwamishinan Ayyuka aka yi su, don haka za a zuba ido a ga ko Abba zai ci-gaba da irin wadannan ayyukan ne.
Wani abu da ake dakon ganin ko Abba zai ci-gaba da yi shi ne irin yadda Kwankwaso ya yi ta bai wa matasa damar zuwa karatu kasashen waje a lokacin da yake gwamna.
Sannan mutane sun zuba ido don ganin wadanda zai zaba a tafiyar da gwamnatinsa, musamman idan aka yi la'akari da dumbin zakakuran matasa da suka taimaka wajen nasararsa.
A gefe guda, akwai kalubalen matsalar tsaro na fashin waya da har yake sanadin mutuwar mutane sosai a Kano. Za a zuba ido don ganin yadda zai shawo kan lamarin.
Kazalika masu sharhi na ganin mutane ba za su dauke ido ba kan yadda dangantakar Abba Gida-Gida da ubangidansa a siyasa, Kwankwaso, za ta ci gaba da tafiya.
Dauda Lawal: Yaya za a yi a Zamfara?
Wani sabon gwamnan da nasararsa ta ja hankalin jama’a shi ne Dauwa Lawal na jam’iyyar PDP mai adawa, wanda ya kayar da Gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara.
Dauda ya yi nasara ne da kuri’u 377,726, yayin da Bello Matawalle ya samu kuri’u 311,976.
Dauda, wanda tsohon ma’aikacin banki ne, ya zama mutum na biyu da ya taba lashe zabe a karkashin jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara.
Shi ma Gwamna Matawallen a da dan jam’iyyar PDP ne, amma daga baya ya koma jam'iyyar APC.
Da zarar ya sha ratsuwa, kallo zai koma kan Dauda Lawal domin ganin yadda zai gudanar da mulki a jihar ta Zamfara.
Za a so a ga yadda mulkinsa zai bambanta da na Bello Matawalle da ya kayar a zabe.
Wani muhimmin bangaren da za a mayar da hankali shi ne wajen ganin yadda sabon gwamnan zai tunkari matsalar tsaron da jihar ke fama da ita.
Za a kuma so a ga irin hanyoyin da sabon gwamnan zai bi wajen gudanar da ayyukan more rayuwa a jihar.
Sannan watakila za a ga ko shi ma zai bi sahun Matawalle na barin jam'iyyar da ya yi nasara a karkashinta ya koma jam'iyya mai-ci a matakin tarayya.
Me zai sauya a Binuwei?
A jihar Binuwei da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, wani wanda ba a sani sosai ba a fagen siyasa ne ya doke jam’iyyar PDP mai mulkin jihar.
Limamin Darikar Katolika Hyacinth Alia na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar da kuri’a 473,933 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Titus Uba ya samu kuri’a 223,913.
Ana ma ganin tasirin limamin na darikar Katolikan na cikin abin da ya sa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya yi nasara a jihar a zaben shugaban kasa.
Mutanen jihar Binuwe da ma ‘yan Nijeriya za su zura ido don ganin yadda sabon gwamnan zai tunkari matsalolin da suka addabi jihar irin matsalar tsaro da kuma rashin biyan albashin malaman makaranta.
Yaya jami’iyyar LP za ta tafiyar da Jihar Abia?
Nasarar da dan takarar gwamnan Jihar Abia na Jam’iyyar LP ya yi ta ja hankalin mutane sosai musamman a kafafen sada zumunta, inda jam’iyyar ta LP take da dimbin magoya baya.
Alex Otti ya yi nasara ne da kuri’a 175,467, yayin da Okey Ahiwe na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 88,529.
An danganta nasarar tasa ne da dan takarar shugabancin kasa na Jam'iyyar Labour Peter Obi.
Jim kadan bayan ayyana Alex a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Abia, sai mutane suka fantsama kan titunan Umuahia, babban birnin jihar suna murnar nasarar da ya samu.
Mutane suna sa ran sabon gwamnan na jihar zai kawo musu ci-gaba irin wanda ba su taba samu ba.
Kazalika mutane daga wajen jihar sun sa ido don ganin kamun ludayin Alex ganin cewa shi kadai ne gwamnan da aka zaba a jam’iyyar LP.
Wace irin rawa Uba Sani zai taka a Jihar Kaduna?
Zaben gwamnan Jihar Kaduna na daya daga cikin zabakun da aka fafata sosai tsakanin Uba Sani na Jam’iyyar APC da kuma Isa Ashiru na Jamiyyar PDP, kafin a sami wanda ya yi nasara.
Uba Sani ya samu kuri’a 730,002 yayin da Isa Ashiru ya samu kuri’a 719,196.
Zaben na gwamnan Jihar Kaduna ya kasance wani zabe da yake cike da rashin tabbas har sai lokacin da aka sanar da sakamakonsa.
Ganin cewa Uba Sani ya kasance mutumin da gwamnan jihar Kaduna mai barin gado, Nasir El Rufai ya so ya gaje shi, mutane za su sa isa ido don ganin ko zai ci gaba da irin salon El Rufai.
Za kuma a zura ido don ganin yadda dangantaka za ta kasance tsakanin El Rufai da sabon gwamnan bayan ya kama aiki.
Sannan za a so ganin kamun ludayin Uba Sani na yadda zai tunkari matsalar tsaro da jihar ke ta fama da ita.