Bola Tinubu zai sha rantsuwa a wani bikin da za a yi a Abuja/Hoto:Fadar Shugaban Nijeriya

Rundunar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta ce ta bankado shirin wasu masu son ta da zaune-tsaye da ke son katse shirin mika mulki ranar 29 ga watan Mayu a wasu sassan kasar.

Wata sanarwar da kakakin rundunar, Peter Afunanya ya sanya wa hannu ta ce burin masu wannan shirin shi ne hana zaman lafiyar da jami’an tsaro ke son tabbatarwa a lokacin bikin mika mulkin.

Hari wa yau sanarwar ta gargadi wadanda ba a gayyata ba su kaurace wa wuraren da aka kebe a lokacin mika mulkin.

Kazalika sanarwar ta nemi mutanen su guji yada labaran karya da kuma labarai na son rai da ka iya tayar da hankali.

DSS ta bankado yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya

A watan Maris din da ya gabata ma, DSS ta bayyana cewa ta bankado yunkurin da wasu manyan masu ruwa da tsaki a fagen siyasa suke yi na ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya.

Ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ga zababben Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a wani bikin da za a yi a Abuja babban birnin kasar.

Sannan za a yi bikin mika mulki ga gwamnoni a jihohi 31 cikin 36 na kasar duk a ranar.

TRT Afrika da abokan hulda