A ranar 29 ga watan Mayu Elrufai zai mika mulki ga zababben gwamnan Malam Uba Sani. Hoto/Nasir El Rufai

Gwamna Malam Nasiru Elrufai ya bayyana irin nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamnan Jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya.

A wata tattaunawa ta bankwana da gwamnan jihar ya yi da gidan talabijin din jihar wato KSMC, gwamnan ya yi godiya ga jama’ar Jihar Kaduna kan damar da suka ba shi tare kuma da fadin yadda tafiyar ta kasance.

A ranar 29 ga watan Mayu ne zai mika mulkin jihar ga zababben gwamnan Malam Uba Sani. Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da gwamnan mai barin gado ya bayyana a yayin tattaunawar:

'Mun yi tsari a Kaduna har zuwa shekarar 2050'

Elrufai ya bayyana cewa sun yi tsarin ne tun daga 2018 har zuwa 2050. Hoto/ Nasir El Rufai

Gwamna Elrufai ya bayyana cewa a tsawon mulkinsa, sun yi tsarin ayyuka da za a ci gaba da tafiyarwa har zuwa shekarar 2050.

“Duka tsare-tsaren sunan nan, wanda kawai za ka yi ka dauka ka bi abin da aka tsara, idan akwai wani gyara da za a yi sai a gyara,” in ji Gwamna Elrufai.

“Wannan tsarin ba wai na hanyoyi ba ne kadai domin mutane sun fi ganin hanyoyi, amma tsari ne wanda baya ga hanyoyi akwai kasuwanni akwai wuraren ayyuka wato masana’antu da ofisoshi da wuraren sayen kayayyaki.

Duka an saka su a wannan tsari daga 2018 har zuwa 2050, kuma duk wanda yake so ya bi wannan tsarin zai ga ci gaban Jihar Kaduna.

Ma’aikata daya da ke samar da akalla biliyan 12 a shekara

A cikin hirar da Gwamnan Jihar Kaduna ya yi, ya bayyana cewa ma’aikatar kula da filaye da safiyo wadda suka sauya ta koma KADGIS a halin yanzu tana samar wa jihar kudaden shiga masu dumbin yawa.

Ya bayyana cewa sakamakon garambawul da suka yi wa ma’aikatar da kuma irin sabbin tsare-tsare da suka kawo, akwai akalla jihohin Nijeriya bakwai da suke son daukar tsarin KADGIS.

Ba na neman mukami a gwamnatin Tinubu - Elrufai

“A shekara daya idan ba mu tara kudi daga KADGIS ba, mu tara biliyan 12, wato kowane wata muna samun kusan naira biliyan daya daga KADGIS kawai,” in ji gwamnan.

Ya bayyana cewa a gwamnatocin baya kudin da ma’aikatar kula da filaye da safiyo ke samarwa a wata ba ya wuce miliyan 100.

Ya kuma bayyana cewa a baya idan mutum yana son sahihan takardun fili ko kadararsa, sai ya dauki fiye da shekara uku yana jira, amma a halin yanzu cikin watanni ko kwanaki mutum zai iya samu.

'Mun yi aiki a duka gundumomin Kaduna'

Gwamnan Jihar Kaduna ya yi karin bayani kan korafe-korafen da ake yi kan cewa a tsawon mulkinsa na shekara takwas, a cikin kwaryar Jihar Kaduna kawai ya yi aiki.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi aiki a duka gundumomi da ke cikin jihar.

“Babu gunduma a Jihar Kaduna da ba mu gyara asibiti ba, babu gunduma da ba mu gyara makarantu ba, babu karamar hukumar da ba mu bayar da kwangilar a yi hanyoyi na kilomita goma ba,” in ji Elrufai.

Ya bayyana cewa kan batun hanyoyin akwai wuraren da ba a samu an yi su ba sakamakon matsalolin tsaro inda ya bayar da misali da Zangon Kataf.

“A kauyuka, mun yi titi kusan kilomita 172 domin duk inda muka ga ana da amfanin gona babu hanyar da za a kawo shi kasuwa, za mu je mu yi hanya,” in ji gwamnan

A ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne Gwamna Nasir zai sauka daga mulki bayan shafe shekara takwas, inda zai mika wa Malam Uba Sani na jam'iyyarsa ta APC wanda ya lashe zaben watan Maris din 2023.

TRT Afrika