Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama a rashin tsaro a Nijeriya./Hoto: Rundunar Sojin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun ceto mutum 24 da 'yan fashin daji suka sace a jihar Zamfara da ke arewacin kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafukan sada zumunta na rundunar ta ce an ceto mutanen ne da sanyin safiyar yau Juma'a.

Sojoji sun ceto mutanen ne, da suka hada da wani jariri ''bayan an yi ba-ta-kashi da kasurguman 'yan fashin daji a kauyen Kabugu Lamba da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara," in ji sanarwar.

Babu cikakken bayani game da yadda aka sace mutanen. Amma hotunan da rundunar sojin ta wallafa sun nuna su cikin mawuyacin hali.

Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Nijeriya inda 'yan fashin daji ke sace mutane domin karbar kudin fansa.

Satar dalibai

'Yan fashin suna bin mutane gida ko su tare kan hanya ko shiga makarantu domin sace dalibai. Kazalika suna sace dabbobi.

Jami'an tsaron Nijeriya sun yi nasarar ceto daruruwan mutanen da aka sace a shekarun baya bayan nan inda suke kai samame ta jiragen yaki kan maboyar 'yan fashin daji a arewacin kasar.

Shugaban kasar Bola Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da daukar matakan dakile matsalolin tsaron kasar bayan mutumin da ya gada tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya taka tasa rawar wajen magance matsalar.

TRT Afrika