Zamfara ta dade tana fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda suke kashe mutane su sace dalibai da jama'ar gari don karbar kudin fansa./Hoto: Reuters

'Yan bindiga sun kashe akalla mutum 34, ciki har da sojoji bakwai a wani hari da suka kai jihar Zamfara, a cewar wani shugaban bijilanti da mazauna yankin.

Sun kai harin ne a kauyen Dan Gulbi da ke karamar hukumar Maru ranar Litinin da la'asar ko da yake sai yanzu bayanai suke fitowa kan lamarin, in ji Ismail Magaji, shugaban bijilanti na kauyen, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Lawali Zonai, wani mazaunin kauyen, ya ce "an kashe farar-hula 27 a harin da 'yan bindiga suka kawo yayin da aka kashe sojoji bakwai a harin kwanton-bauna a lokacin da suke kan hanyarsu ta kawo mana agaji."

Kakakin rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen jihar Zamfara bai amsa kiran wayar da aka yi masa don karin haske game da batun ba.

Zamfara ta dade tana fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda suke kashe mutane su sace dalibai da jama'ar gari don karbar kudin fansa.

Reuters