Malawi

Hukumomi a Malawi sun kaddamar da bincike don gano musabbabin da ya jawo gobarar da ta faru a wani ginin gwamnati a babban birnin kasar, Lilongwe, inda ta kona muhimman bayanai.

Gobarar ta kama ne a hawa na shida da na bakwai na ginin da ma’ajiyar bayanan filaye da kasa, sashen bayar da kwangila na gwamnati da sashen shari’a.

Ministan Yada Labarai na Malawi Moses Kunkuyu ya bayyana cewa gobarar da ta kama da tsakar daren Asabar din karshen makon da ya gabata, ta mamayi hawa na shida da na bakwai na ginin da ma’ajiyar bayanan filaye da kasa, inda sashen bayar da kwangila na gwamnati da sashen shari’a suke.

Bayanan da kafafan yada labarai na kasar suka fitar sun bayyana cewa ana fargabar muhimman takardu da ke dauke da bayanan mallakar gidaje da filaye da mika kadarori tsakanin mutane, amma gwamnatin ta ce ana ajiye dukkan bayanan ma’aikatar kasa da filaye a yanar gizo.

“Kar jama'ar kasa su damu kan duk wani zargi na rasa bayanai saboda mummunar gobarar da ta afku”, in ji Kunkuyu.

Ya ce, jami’an tsaro da suka hada da na ‘yan sanda ne suke gudanar da binciken, kuma za a bayyana wa jama’a sakamakon da aka samu bayan kammala binciken.

Ba wannan ne karo na farko da ginin ya kama da wuta ba. A 2019 ma gobara ta kama ginin. Masu amfani da shafukan sada zumunta na muhawara kan akwai kitimurmura game da gobarar.

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera da aka zaba a 2020 kan manufarsa ta yaki da cin hanci da rashawa, na fama da zarge-zargen ayyukan cin hanci da rashawa da gaza hukunta masu aikata hakan a gwamnatinsa.

Mataimakinsa Saulos Chilima na fuskantar tuhuma kan cin hanci da rashawa bisa zargin sa da karbar kudi don bayar da kwangila.

Chilima ya musanta aikata wani laifi.

TRT Afrika