'Yan tawayen M23 sun sanar da  tsagaita wuta a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

'Yan tawayen M23 sun sanar da  tsagaita wuta a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

'Yan tawayen sun jaddada buƙatarsu ta karewa da kuma kiyaye fararen-hula a duk inda suke.
'Yan tawayen M23 na samun goyon bayan dakarun kusan 4,000 daga Rwanda, kamar yadda ƙwararru na Majalisar Ɗinkin Duniya suka bayyana. / Hoto: Reuters Archive

'Yan tawayen M23 waɗanda suka ƙwace wani babban birni a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun sanar da tsagaita wuta, inda suka ce sun yi haka ne saboda jinƙai, amma babu wasu alamu da ke nuna za su haƙura da birnin Goma, birnin da ke da ma'adinai na tiriliyoyin daloli.

Sanarwar na zuwa ne a ranar Litinin, jim kaɗan bayan Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa aƙalla mutum 900 sun rasu a makon da ya gabata sakamakon yaƙin da ake yi tsakanin 'yan tawayen M23 da kuma dakarun ƙasar Kongo bayan 'yan tawayen sun ƙwace iko da birnin Goma, birni mai mutum miliyan biyu.

Daga baya an bayar da rahoton cewa 'yan tawayen sun ci gaba da tafiya zuwa babban birnin wani lardi, wato birnin Bukavu, inda suka lashi takobin ci gaba da yin gaba har zuwa Kinshasa, babban birnin Kongo.

"Ya kamata a sani cewa ba mu da wata manufa ta ƙwace iko da Bukavu da sauran yankuna. Sai dai muna ƙara jaddada sadaukarwamu wurin karewa da kiyaye fararen hula," kamar yadda mai magana da yawun 'yan tawayen M23 Lawrence Kanyuka ya bayyana a wata sanarwa.

Sai dai zuwa yanzu babu wani jawabi daga gwamnatin DRC game da wannan batun.

TRT World