Masu zanga-zangar suna rike da tuta mai rubutun a "dakatar da wariyar launin fata, dakatar da ƙyamar Musulunci" a gangamin nuna adawa na kungiyoyi daban-daban a Paris a ranar 21 ga Afrilu, 2024. / Photo: AFP      

Kimanin mutum 2,000 ne suka taru a birnin Paris don nuna adawa da wariyar launin fata da ƙyamar addinin Musulunci, da kuma cin zarafin da ƴan sanda suke yi a Faransa yayin da suke nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza waɗanda ke fama da matsala da tashin hankali na jinƙai.

Masu zanga- zangar sun riƙe tutar Falasdinu tare da sanya ire-iren tufafi ko lullubi na kasar yayin da suke rera taken adawa da abubuwan da suke faruwa a Gaza a ranar Lahadi.

Kazalika sun baje alluna da ke dauke da rubutun "A daina nuna wariyar launin fata, a daina ƙyamar Musulunci," "Ya'yanmu na cikin hadari,"

"A daina kisan kare dangi a Gaza" da kuma "mu na adawa da mulkin mallaka da yahudawa ke yi."

Manya-manyan kungiyoyin masu ra'ayin riƙau na Yellow Vest na Faransa da kuma 'yan jam'iyyar La France Insoumise (Faransa Unbowed) da kuma baƙaƙen mutane bakin haure ne suka halarci gangamin.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar ƴan asalin Afirka sun nuna adawarsu ta hanyar raye-raye da kade-kade na wakokin cikin gida.

Kazalika jama’a sun rera taken tunawa da wani matashi ɗan asalin Arewacin Afirka da aka harbe har lahira a shekarar da ta gabata a yayin binciken ƴan sanda a kan hanya.

TRT World