Adadin Falasdinawan da suka mutu  ya kai 40,878 a yakin Isra'ila na Gaza / Photo: Reuters / Photo: AFP

Alhamis, 25 ga Satumban 2024

1350 GMT — Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce akalla mutane 40,878 ne Isra'ila ta kashe a yakin da take yi a yankin Falasdinu, wanda yanzu ya kusa wata 12.

Adadin wadanda suka mutu ya hada da mutuwar mutane 17 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar alkaluman ma'aikatar, wanda kuma ya bayyana mutane 94,454 da suka samu raunuka a Gaza tun farkon mamayar Isra'ila bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

1226 GMT — Falasdinawa 8 ne suka mutu a sabon harin da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza

Akalla Falasdinawa takwas ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, a cewar majiyoyin lafiya da shaidu.

Wata majiyar lafiya ta ce mutane uku ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin saman Isra'ila mara matuki ya kai hari a kusa da makarantar Zeitoun Shahidai a kudu maso gabashin Birnin Gaza.

Wata majiyar lafiya ta sanar da cewa, an kashe ƙarin mutane hudu tare da jikkata wasu da dama a harin da Isra'ila ta kai kan tantunan 'yan gudun hijira a asibitin shahidan al-Aqsa da ke tsakiyar birnin Deir al-Balah.

Wata majiya ta ce wani harin da Isra'ila ta kai kan wani tanti na 'yan gudun hijira ya kashe akalla mutum daya a yammacin Khan Younis a kudancin Gaza.

Hukumar tsaron farar hula ta ce, an kuma bayar da rahoton jikkata mutane da dama a wani harin da jirgin sama mara matuki ya kai kan wani wurin sana'ar dinki a wani gida da ke arewacin birnin Gaza.

Hakazalika sojojin Isra'ila sun rushe wasu gine-gine da dama a gabashin birnin Gaza da kuma tsakiyar Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.

0803 GMT — Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sun kashe Falasɗinawa 39

Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankin arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya kai 39 tun daga makon da ya wuce, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta faɗa.

Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sun kashe Falasɗinawa 39.

"Yara takwas da tsofaffi biyu na daga cikin mutanen da aka kashe, in ji sanarwar ma'aikatar. tana mai cewa an kuma jikkata wasu mutum 145.

A birnin Jenin ne aka fi yawan waɗanda suka mutu inda aka kashe mutum 19, sai kuma birnin Tubas da aka kashe mutum 10, a cewar ma'aikatar.

2100 GMT — Amurka ta sha alwashin samar da tsaro ga Isra'ila idan ta bar Philadelphi Corridor

Wani babban jami'in Amurka ya ce idan sojojin Isra'ila suka janye daga yankin Philadelphi Corridor, wani dan karamin fili da ke tsakanin Masar da Falasdinu da aka fi sani da Saladin Axis, "akwai abubuwan da Amurka za ta iya yi [domin] bai wa Isra'ila cikakken bayanin tsaron da take bukata."

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Washington DC, jami'in ya ce Amurka tana da kwarin gwiwa game da shirye-shiryen tsaro a kusa da titin, wanda firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke son ci gaba da kasancewa karkashin ikon Isra'ila.

Hakan na zuwa ne bayan Netanyahu ya jaddada ƙin amincewarsa na janyewa daga titin, yana mai ikirarin ba tare da wata hujja ba cewa kungiyar gwagwarmayar Hamas za ta iya kwashe mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su daga kudancin Gaza.

Titin Philadelphi ya kasance cibiyar cece-kuce a tattaunawar Isra'ila da Falasdinu. Masu suka sun ce ƙin janyewar Netanyahu daga titin ya dagula yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas.

2200 GMT — Babu buƙatar sabbin shawarwarin sulhu: Hamas

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce babu bukatar wata sabuwar shawarar tsagaita wuta, tana mai cewa lokaci ya yi da za a matsa lamba kan Isra'ila.

Hamas ta caccaki Netanyahu, tana mai cewa matakin da Firaministan Isra'ila ya yanke na ƙin janye sojoji daga Philadelphi Corridor na da nufin daƙile yarjejeniyar sulhu da musayar fursunoni.

TRT Afrika da abokan hulda