Laraba, 4 ga Satumba, 2024
1241 GMT — Masu shiga tsakani za su gabatar da 'tsarin sulhu' don tsagaita wuta a Gaza
Ana sa ran masu shiga tsakani za su gabatar da "tsarin sulhu" na tsagaita wuta a Gaza da kuma musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas, a cewar kafar yada labaran Isra'ila.
Kafar yada labarai ta Isra'ila KAN ta ce za a gabatar da shirin a ranar Juma'a, ba tare da bayar da cikakkun bayanai kan abubuwan da ke cikinsa ba.
KAN ya ce shugaban Mossad David Barnea ya sanar da masu shiga tsakani cewa Isra'ila a shirye take ta janye daga hanyar Philadelphi Corridor da ke kan iyakar Gaza da Masar a mataki na biyu na shirin tsagaita wuta.
Barnea ya isar da wannan sako ga masu shiga tsakani duk da furucin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi cewa Isra'ila za ta ci gaba da kula da harkokin tsaro.
0159 GMT — Ƙarin alluran riga-kafin cutar shan inna guda 350,000 sun isa Gaza, in ji Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu.
Alluran sun isa yankin da aka mamaye a lokacin da ake ci gaba da gangamin yin allurar da kuma fuskantar hare-hare daga Isra’ila.
“Ƙarin alluran cutar shan inna 350,000 sun iso Zirin Gaza a yammacin Talata, kuma an ajijye su a akwatuna masu sanyi da ke Ma’aikatar Lafiya a Deyr al-Balah,” in ji Ministan Lafiya na Falasɗinu Abu Ramadan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu an kawo adadin alluran miliyan 1.6, kuma sun isa a yi wa dukkan yara ƙanana da ba su wuce shekara 10 ba, kuma kowane yaro zai karɓi alluran guda biyu.
A ranar Talata wani hari ta sama da Isra’ila ta kai Gaza ya kashe Falasɗinawa bakwai tare da jikkata wasu 30, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya sanar.
Harin ya samu wani wani gini da ke kusa da filin shakatawa a Gaza, inda fararen-hula biyar da suka haɗa da yaro daya suka mutu.
Haka zalika, dakarun Isra’ila sun kutsa kai Kwalejin Noma tare da kasha fararen-hula biyu da jikkata wasu 30. A wannan lokaci dai, jirgin yaƙi marar matuki na Isra’ila ya kai hari kan Falasɗinawa a unguwar Shujaiya inda ya jikkata mutane.
0146 GMT —Mayaƙan Al-Qassam sun fitar da bidiyon wani fursunan yaƙi ɗan Isra’ila da aka kashe yana sukar Netanyahu
Mayaƙan Al-Qassam, reshen soji na ƙungiyar Hamas, sun saki wani bidiyo da ke nuna wani ɗan Isra'ila da suka yi garkuwa da shi yana sukar Netanyahu, bayan da Isra’ila ta bayyana cewa yana cikin gawarwaki biyar da aka gano a Gaza.
A cikin bidiyon na mintuna biyu, Ori Danino mai shekara 25 ya soki gwamnatin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa gaza kuɓutar da su. Ya yi gargaɗi cewa ci gaba da kai hare-haren bama-bamai yankin da Isra’ila ke yi zai kasha dukkan fursunonin.
"Jefa bama-bamai da harba bindigu daga sojojin isra’ila bai dakata ba.” In ji shi.
Da yake bayani ga gwamnatin Isra’ila da majalisar ministocin da ke yaki, y ace “A yanzu kuna kokarin kashe mu daya bayan daya ta hari ta sama bayan gaza kubutar da mu da kuma yi.”
0115 GMT — Sojojin Isra’ila sun yi gargaɗin cewa hare-hare a Gaza ba tare da yarjejeniya ba na jefa rayuwar fursunonin yaƙi cikin hatsari
Sojojin Isra’ila sun gargaɗi gwamnati cewar idan har ba a cim ma yarjejeniya da Hamas ba, duk wani hari babba da za a kai Gaza zai janyo kashe fursunonin yaƙi 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a Gaza, in ji kafar watsa labarai ta ƙasar.
“Sojojin Isra’ila sun bayyana ƙarara ga gwamnati cewa matuƙar ba a cim ma matsaya da Hamas ba, to dole a fahimci cewa duk wani hari babba da za a kai Gaza zai jefa rayuwar fursunonin yaƙi cikin hatsari,” in ji jaridar Yedinoth Ahronoth da ke Isra’ila.
Jaridar ta ambato wani jami’in soji da aka ɓoye sunansa yana cewa “Majalisar ministoci ce za ta yanke hukuncin ɗaukar alhakin rayuwar waɗanda aka yi garkuwar da su.”
Rahoton ya ce sojojin na ci gaba da gargaɗin gwamnati.