Juma'a 6 ga watan Satumban 2024
1500 GMT — Hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai sun kashe akalla Falasdinawa 27 a fadin Gaza, in ji ma’aikatan lafiya, yayin da jami’an kiwon lafiya suka sake ci gaba da yi wa dubban yara allurar rigakafin cutar shan inna a yankin.
A Nuseirat daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira takwas masu dimbin tarihi a yankin, wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya kashe mata biyu da kananan yara biyu, yayin da wasu mutane takwas suka mutu a wasu hare-hare ta sama guda biyu da aka kai a birnin Gaza, in ji likitocin.
Sauran an kashe su ne a hare-haren da aka kai a yankin, in ji su.
1218 GMT — Mai shigar da ƙara na Kotun Duniya ya kare matakinsu na ba da sammacin kama Netanyahu
Babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ya kare matakinsu na sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, yana mai cewa dole ne a ga an yi adalci.
A wata hira da ya yi da BBC, Karim Khan ya ce yana da muhimmanci a nuna cewa kotun za ta rike dukkan kasashen duniya daidai gwargwado dangane da laifukan yaki da ake zarginsu da aikatawa, yana mai maraba da matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na janye adawarta da sammacin kama shi.
A watan Yuli ne dai gwamnatin Birtaniya ta janye adawarta da kotun ta ICC da ke neman a kama Netanyahu.
0410 GMT — Dakarun Isra'ila sun fice daga Jenin bayan shafe kwana 10 suna kai farmaki
Sojojin Isra'ila sun janye daga birnin Jenin da kuma wani sansanin 'yan gudun hijira da ke can, bayan shafe kwanaki 10 na "tashin hankali", in ji kamfanin dillancin labarai na Falasdinu (WAFA).
An kashe mutum 21 a cikin birnin da sansanin, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a cikin wata sanarwa.
Wani shaida na Reuters ya ce sojojin Isra'ila sun yi ɓarna mai yawa a kan ababen more rayuwa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin Facebook, ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta zargi Isra'ila da yin mummunar ɓarna a yankin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye kamar yadda ta yi a Gaza, kamar yadda aka gani a garuruwan Jenin da Tulkarem da kuma sansanonin 'yan gudun hijira da ke can.
0552 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan wani matashin Falasdinawa a Ramallah
Sojojin Isra'ila sun kai hari kan wani matashi a kauyen Deir Abu Mashal da ke arewacin Ramallah, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA.
An kai harin ne a kauyen Shuqba a wani shingen bincike na wucin gadi da sojojin Isra'ila suka kafa, kamar yadda majiyoyin kasar suka bayyana.
Harin da sojojin Isra'ila suka kai kan Bilal Rabah Dar Atta ya yi sanadiyar karya masa yatsunsa. Nan take aka kai shi wani asibiti domin yi masa magani.
1951 GMT — Israilawa sun yi gangamin adawa da Netanyahu ɗauke da akwatunan gawa don yi masa a kan yaƙin Gaza
Ɗaruruwan Isra’ilawa ne suka yi zanga-zangar lumana a kan titunan birnin Tel Aviv dauke da akwatunan gawa guda 27 don wakiltar mutum 27 da sojojin Isra’ila suka yi garkuwa da su a cikin watanni kusan 11 da suka gabata na kisan gilla a Gaza.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki a cikin manyan tituna a birnin Tel Aviv da daddare, inda suka rika buga kararrawa a kan tituna.
Kasar dai na cikin tashin hankali ne sakamakon gano gawarwakin wasu ‘yan Isra’ila shida da aka yi garkuwa da su, wadanda Hamas ta ce an kashe su ne a hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kai.
"Benjamin Netanyahu, Firaminista, ya yanke wa 'yar uwata Carmel hukuncin kisa, da ita da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su," in ji Gil Dickmann, ɗan uwan Carmel Gat, daya daga cikin mutane shida da aka yi garkuwa da su, kuma aka gano gawarta.
"Gwamnati ta yi watsi da ita har ta mutu, za ta iya dawo da ita, kwanaki 327 tana can, a Gaza, a cikin garkuwa, akwai damar 327 da za a dawo da ita kuma an rasa kowane daya."
A cikin bayanan da suka yi cikin fusata a bainar jama'a, iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su sun zargi Netanyahu da dakile wata yarjejeniya da kuma yuwuwar sadaukar da rayukan 'yan uwansu saboda burikansa na siyasa.