Kisan ƙare dangin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 447, kuma ya kashe aƙalla Falasdinawa 45,399 tare da jikkata 107,940.

Alhamis, 26 ga Disamban 2024

1428 GMT — Za a iya ɗaukar matakin shari'a a kan Amurka da Jamus saboda su ke bai wa Isra'ila kashi 99% na makamai: Wakilin MDD

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin dan'adam da yaki da ta'addanci ya ce za a iya daukar matakin shari'a kan Amurka da Jamus yayin da suke samar da kashi 99 na makaman Isra'ila.

Da yake lura da cewa akwai ‘yan kadan’ na kasashen da a halin yanzu suke bai wa Isra’ila makamai, Ben Saul ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, kusan kashi 69 na makamai da alburusai da Isra’ila ke samu, Amurka ce ke ba ta, sai kuma Jamus da take ba ta kusan kashi 30 cikin 100.

"Kowace kasa na da hakki a karkashin dokokin kasa da kasa na tabbatar da cewa ba su kai wa wata kasa makamai ba inda za a yi amfani da wadannan makaman wajen keta dokokin jinƙai na kasa da kasa," in ji shi.

1354 GMT — Iyalan Isra'ilawan da ake garkuwa da su a Gaza sun yi barazana maka Netanyahu a kotu kan ƙin bin yarjejeniyar musayar fursunoni

Iyalan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a Gaza sun yi barazanar daukar matakin shari'a kan Firaminista Benjamin Netanyahu, tare da zarginsa da hana yarjejeniyar musayar fursunoni da Falasdinawa.

"Za mu shigar da kara kotu idan kuka dage wajen yin watsi da 'yan'uwanmu a hannun Hamas," in ji iyalan a cikin wata wasika ga Netanyahu da jaridar Isra'ila Yedioth Ahronoth ta ruwaito.

Wasikar ta zargi firaministan Isra'ila da hana yunkurin cim ma yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas.

"Ƙin kawo karshen yakin yana zama sadaukar da rayukan wadanda aka yi garkuwa da su kuma yana rage musu damar dawowa da rai," in ji shi.

1226 GMT — An tilasta wa jirgin ruwan Amurka ja da baya a Bahar Maliya bayan wani hari: Houthis

Kungiyar Houthi ta Yemen ta yi ikirarin tilasta wa wani jirgin yakin Amurka ja da baya a Tekun Bahar Maliya bayan wani harin da jiragen yaki marasa matuka suka kai.

Shafin intanet mai suna September 26 da ke da alaka da ma'aikatar tsaro ta Houthi, ta ce an tilasta wa jirgin ruwan Amurka USS Harry S. Truman ja da baya a arewa a cikin tekun Bahar Maliya zuwa mashigar Suez na Masar bayan wani hari a farkon makon nan.

Shafin intanet na kasar Yemen ya bayyana cewa, hotunan tauraron dan'adam sun nuna jirgin na Amurka yana barin tekun kasar Yemen.

TRT World