Alhamis, 3 ga Oktoban 2024
1627 GMT — Wata 'yar siyasar Sifaniya ta zargi Isra'ila da amfani da bam mai ƙona mutum har cikin ƙashi a kan 'yan Lebanon
Irene Montero 'yar jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi ta Sifaniya, Podemos, ta zargi Isra'ila da amfani da wani mugun bam mai sinadarin da ke ƙona jikin mutum har cikin ƙashi a kan 'yan Lebanon.
"Bam mai sinadarin white phosphorus yana jawo muguwar ƙuna a jikin mutum mai isa har cikin ƙashi," kamar yadda ta wallafa a shafinta na X. Ta ƙara da cewa: Isra'ila na kai hare-hare Beirut da makaman da aka haramta." Montero ta bayyana jami'an Isra'ila da cewa "masu aikata miyagun laifuka ne kuma 'yan ta'adda ne"
Ta ce "Masu fada a ji a Turai za su mayar da martani kan wannan hadin kai da kasar Isra'ila ke yi na kisan kare dangi."
1359 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya 28 a Lebanon cikin sa'o'i 24 — WHO
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya ce an ma’aikatan lafiya 28 aka kashe a cikin sai’o’i 24 da suka wuce a Lebanon, inda Isra’ila ta kai hare-hare ta sama tare da tura sojojinta cikin rikici da ke ci gaba da fadada.
"Sauran ma'aikatan lafiya da dama ba sa bakin aikinsu kuma sun tsere daga wuraren da suke aiki saboda tashin bama-bamai," kamar yadda Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa taron manema labarai ta intanet.
"Wannan yana matuƙar kawo tsaiko a hanyoyin takaita tashin hanakali da kuma ci gaban ayyukan kiwon lafiya," in ji shi.
1101 GMT — Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa ta yi taron gaggawa kan yaƙin da Isra'ila ke yi a Lebanon
Kungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa ta gudanar da wani taron gaggawa a birnin Alkahira, inda ta tattauna kan hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa ƙasar Lebanon, a daidai lokacin da rikicin yankin ke ƙara ƙamari.
Iraki ta kira taron ne domin tattaunawa kan "ta'azzarar hare-haren da sojojin Isra'ila suke yi a kan Lebanon, da irin yadda take yi da kuma hanyoyin samar da magunguna da abinci ga waɗanda abin ya shafa," a cewar kamfanin dillancin labarai na Masar MENA.
Mahalarta taron za su tattauna batun yin kira ga al'ummar duniya "domin su tsaya tare da al'ummar Lebanon tare da ba da gudunmawa tare da kungiyoyin kasa da kasa don isar da agajin gaggawa cikin gaggawa," in ji MENA.
0606 GMT — Mayaƙan Houthi na Yemen sun yi iƙirarin kai hari a Tel Aviv
Mayaƙan Houthi na Yemen waɗanda ke samun goyon bayan Iran sun ce sun ƙaddamar da hari da jirgi mara matuƙi a Tel Aviv, ko da yake hukumomin Isra'ila ba su tabbatar da hakan ba.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta Houthi ta fitar, ta ce mayaƙanta sun "kai harin soji inda suka nufi yankin Jaffa (Tel Aviv) a yankin Falasɗinu da aka mamaye da wasu jirage marasa matuƙa na Jaffa".
"An cim ma burin kai harin cikin nasara domin kuwa jiragen marasa matuƙa sun isa inda aka harba su ba tare da maƙiya sun tunkare su ko harbo su ƙasa ba."
0625 GMT — Japan ta tura jiragen soji don kwashe 'yan ƙasarta daga Lebanon
Japan ta tura jiragen soji biyu zuwa Jordan da Girka domin shirin kwashe 'yan ƙasarta daga Lebanon, a cewar wasu rahotanni na kafofin watsa labaran ƙasar.
Rundunar Sojojin Sama ta Ƙasa ta tura jirage biyu samfurin C-2 daga Filin Jirgin Saman Miho Air da ke lardin Tottori na Japan, domin shirin kwashe 'yan ƙasar daga Lebanon, in ji kafar watsa labarai ta Kyodo News, wadda ta ambato Ma'aikatar Tsaron ƙasar.
Akwai 'yan ƙasar Japan 50 da ke zaune a Lebanon.
2331 GMT — Isra’ila ta kai harin bam a tsakiyar birnin Beirut da sanyin safiyar Alhamis, inda ta kashe akalla mutane shida, bayan da sojojinta masu mamaya suka ga mafi munin rana a gagarumin artabun da ba su taba irinsa ba a fagen daga tsakaninsu da kungiyar Hezbollah ta Lebanon a cikin shekara guda.
Shaidu sun ba da rahoton jin karar fashewar wani katon bam kuma wata majiyar tsaro ta ce Isra'ila ta kai hari kan wani gini da ke tsakiyar birnin Beirut a unguwar Bachoura da ke kusa da majalisar dokokin kasar, harin da Isra'ila ta kai a kusa da ofishin gwamnatin Lebanon.
Akalla mutum shida ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata, in ji jami'an kiwon lafiya na kasar Lebanon.
Wani hoto da ake yadawa a kafofin WhatsApp a kasar Lebanon ya nuna wani gini da ya lalace sosai tare da cin wuta a benensa na farko.
Har ila yau, sun kai harin makami mai linzami uku a yankin kudancin Dahiyeh, inda aka kashe shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah a makon da ya gabata, an kuma ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi kamar yadda jami'an tsaron kasar Labanon suka sanar.
Yankunan kudancin kasar sun fuskanci hare-hare sama da goma na Isra'ila a ranar Laraba.
Hukumar kula da bala'o'i ta kasar Lebanon ta fada a baya cewa mutane 1,928 Isra'ila ta kashe a kasar tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
2220 GMT — Isra'ila ta kashe wani Ba'amurke a Lebanon
Gwamnatin Amurka ta ce an kashe wani Ba’amurke dan asalin garin Dearborn a jihar Michigan, a kasar Labanon, inda abokin mutumin da makwabtansa suka ce an kashe shi ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama.
Kakakin Fadar White House ya ce "Muna matukar bakin ciki da rasuwar Kamel Ahmad Jawad, kuma muna mika ta'aziyyarmu ga 'yan uwansa da abokan arziki. Mutuwar tasa wata abar takaici ce, haka ma mutuwar fararen hula da dama a Lebanon."
Tun da farko dai, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, da aka tambaye shi game da rahotannin mutuwar wani Ba'amurke a Lebanon, ya ce: "A fahimtarmu ne cewa mazaunin kasar ne na dindindin bisa tsarin doka, ba wani Ba'amurke ba (wanda aka kashe a Lebanon) amma duk da haka muna mika ta'aziyyarmu ga 'yan uwa."