Aƙalla mutum 50 aka kashe yayin da aka jikkata gomman mutane a wani harin da ‘yan daba ɗauke da makamai suka kai a Kenscoff, wani garin da ke da nisan kilomita 10 (mil 6.2) daga babban birnin Haiti, Port-au-Prince, kamar yadda rahotanni daga ƙasar suka ruwaito.
Harin, da aka siffanta a matsayin “gagarumi” hari na neman ƙwace garin, ya kai ga ƙona gidaje 100, in ji wata ƙungiya mai zaman kanta.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Haiti Michel-Ange Louis Jeune, ya ce dakarun tsaro sun kashe ‘yan bindiga 20 a lokacin harin kuma ya tabbatar da cewa ana ɗaukar matakai na tabbatar da zaman lafiya.
An tura ƙarin dakarun tsaro garin bayan maharan sun nemi fin ƙarfin dakarun tsaron da ke wurin.
Haiti, ƙasa mai jama’a miliyan 11, ta shafe shekaru tana fama da matsaloli na siyasa da tattalin arziki da tsaro.
A halin yanzu ‘yan bindiga suna iko da kimanin kashi 80 cikin 100 na Port-au-Prince, kuma tashin hankali na ci gaba da ƙamari. A shekarar 2024 kaɗai, sama da mutum 5,000 aka kashe a hare-haren da suka jiɓinci daba.
Rashin zaman lafiyar ƙasar ya sa ana yawan samun sauya shugabancin ƙasar.
Firayim minista Ariel Henry ya yi murabus ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 2024 cikin tashin hankali, kuma an naɗa Garry Conille a matsayin magajinsa. Ɗan kasuwa Alix Didier Fils-Aime ne ya maye gurbin Conille ranar 11 ga watan Nuwamba.