Da gangan aka salwantar da rayukan Falasdinawa da dama a ayyukan kai ɗauki da aka shirya domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, in ji ma'aikatar lafiyta a Gaza, batun da Netanyahu bai ambata ba./ Hoto: Reuters

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kare yaƙin kisan kiyashin da ƙasarsa take ci gaba da yi a Gaza wadda ta yi wa ƙawanya, yana mai kira ga Amurka da ta ci gaba da mara wa masu baya a yayin wani jawabi mai zafi da ya gabatar a gaban Majalisa Dokokin Amurka.

Ya kuma ya ba da misali da wani rahoton sirri da ba a tantance ba, kana ya yi watsi da mafi yawan sukar da aka yi wa yaƙin da ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar Falasdinawa tare da lalata Gaza.

Ga ƙarairayi da gaskiyar abubuwan da suka faru:

Ƙarya: "Duk da ire-iren ƙarairayi da kuka ji, yaƙin Gaza yana ɗaya daga cikin wurare mafi ƙaranci da aka yi yaƙi wanda ya haɗa mayaƙa da waɗanda ba 'yan ta'adda ba a tarihin yaƙin birane."

Gaskiya: Adadin waɗanda aka tabbatar sun mutu a Gaza ya kai kusan mutum 40,000, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, wacce ta yi ta yaɗa jerin sunayen mutanen da suka mutu, gami da lambobin tantance su da Isra'ila ta bayar da kuma bayanansu daga yaƙe-yaƙen da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da faruwarsu.

Yawancin waɗanda suka mutu cikin dubban Falasɗinawan mata ne da yara, kuma daga ciki ba kowanne ba ne ya kasance ɗan ta'adda ko ɗan gwagwarmaya ba.

Isra'ila dai ta yi watsi da batun kashe fararen hula, inda ta ɗora alhakin hakan kan ƙungiyar Hamas yayin da adadin mutanen da suka mutu ya karu sosai cikin watanni tara da suka gabata.

Adadin waɗanda suka mutu a zahiri ya zarce yawan adadin da aka fitar a hukumance, al'amarin da hatta gwamnatin Biden ta yarda da shi.

Kazalika mafi yawa daga cikin mutanen da suka mutu suna binne ne a ƙarkashin ɓaraguzan gine-gine a Gaza, ko kuma sojojin Isra'ila sun binne su ne a wasu keɓantatun wurare.

Ƙarya: "Ina ba da shawarar ku saurari Kanal John Spencer, shi ne shugaban Nazarin Yaƙin Birane a yankin West Point, kuma ya yi nazari kan manyan yaƙi na birane, ina nufin a tarihin wannan zamani,' ya min gyara, a'a, a tarihin Isra'ila, in ji shi, ta aiwatar da matakan kariya don hana cutar da fararen hula fiye da kowane soji a tarihi kuma fiye da abin da dokar duniya ta buƙata.''

Gaskiya: Spencer wani manazarci ne na soja wanda shi ne shugaban shirin Nazarin Yakin Birane a West Point. Shahararren mai goyon bayan Isra'ila ne wanda bincikensa kan Gaza ya zama shi kadai a cikin sauran al'umma.

Ƙarairayin da Netanyahu ya shirga, wanda Spencer ya amince da su a shafinsa na X, sun yi hannun riga da kiraye-kirayen da aka yi wa Isra'ila da ta ƙara yin ƙoƙarin daƙile cutar da fararen hula, ciki har da gwamnatin Biden wacce ta kwashe watanni tana kira kan dole a ƙara yin ƙaimi ba don kawai guje wa ƙarin mace-mace ba, amma don inganta yanayin jinƙai a faɗin Gaza.

MDD ta kuma yi kakkausar suka kan yanayin da Isra'ila ta ɗauka a matsayin "yanki masu aminci," a cewar James Elder, mai magana da yawun UNICEF a ranar 16 ga watan Yuli.

''A karkashin dokokin duniya, wurin da za ku kai mutane dole ne ya kasance yana da isassun kayayyaki da za a iya rayuwa kamar - wuraren kiwon lafiya da abinci da kuma ruwa."

A zahiri waɗannan wuraren da suka kira ''masu aminci'' ba su da aminci, ba wai a lokacin da suke tsare daga hare-hare ba ne kawai, amma lokacin da aka cika waɗannan sharuɗɗa na samar da - abinci da ruwa da magunguna da kuma kariya.

Haka kuma, wuraren nan masu aminci da suke faɗa, ƙananan filaye ne ko gefen unguwanni ko dai gidaje da ba a ƙarasa gina su ba, sannan babu ruwa ko kayayyakin amfani balle wuri mai kyau da zai iya kare mutum daga sanyi ko zafi ko kuma ruwan sama.

Kuma a halin yanzu, cikin wani mummunan yanayi ga iyalai da dama a Gaza, wadanda aka tilasta wa shiga yankin Al Mawasi 'mai aminci' ba wai kawai an hana su damar samun wannan damarmaki na ceton rai ba ne, amma an jefa musu bama-bamai har sau uku a cikin makonni shida da suka wuce!"

Kalaman sun biyo bayan kashe mutum 90 a wasu jerin hare-hare da aka kai a yankin Al-Mawasi mai aminci kusa da Rafah.

Ƙarya: "Idan akwai Falasdinawa a Gaza da ba sa samun isasshen abinci, ba don Isra'ila ta toshe musu hanya ba ne, amma don Hamas tana satar musu abinci ne."

Gaskiya: MDD da kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun sha yin suka game da takunkumin da Isra'ila ta ƙaƙaba kan shigar da kayayyakin jinƙai, tare da hana jigilar kayayyaki da zarar motoci suka shiga Gaza, haka kuma Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan motocin da suke koƙarin kai kayayyakin da ake da matukar buƙata.

Wasu jerin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kan ayarin motocin abinci na duniya a ranar 1 ga Afrilu, sun kashe ma'aikata bakwai, kuma ya sanya manyan ƙungiyoyin agaji dakatar da ayyukansu na jinƙai.

A watan Yuni ne, hukumar samar da abinci ta duniya ta dakatar da ayyukanta, bayan da aka kai wa wasu manyan wurin ajiye abinci biyu hari da makamin roka, a wani harin samame da Isra'ila ta yi wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa kusan 300.

Hukumar ta kasance tana gudanar da ayyukan shigar da kayayyaki daga wani mashigin wucin gadi da Amurka ta gina a gaɓar Tekun Gaza don ƙauce wa takunkumin Isra'ila.

Rashin isasshen kayan abinci ya haifar da matsanancin ƙarancin abinci da rashin tsaftataccen ruwa a fadin Gaza.

Wani kwamiti mai wakilai 10 masu zaman kansu a MDD ya faɗa a ranar 9 ga watan Yuni cewa ''babu tantama'' akwai tsananin yunwa a duk fadin Gaza a yanzu.

"Muna shelanta cewa yaƙin da Isra'ila ke yi da gangan da kuma haifar da yunwa a kan al'ummar Falasdinu wani nau'i ne na kisan ƙare dangi wanda ya haifar da tsananin yunwa a faɗin Gaza.

Muna kira ga al'ummar duniya kan su mai da hankali wajen ganin an kai kayayyakin jinƙai ta ƙasa ko ta wane hali, sannan su tabbatar da cewa an kawo karshen harin da Isra'ila ke yi, da kuma tsagaita wuta," in ji su.

Ƙarya: Netanyahu ya yi iƙirarin cewa ''ba a wani samu asarar rayukan fararen hula daga hare-haren Isra'ila a kudancin birnin Rafah na Gaza ba."

Gaskiya: Ikirarin ba wai shaci faɗi ba ne, tsantsar ƙarya ce. Isra'ila ta yi ta kai hare-hare da dama a Rafah waɗanda suka yi sanadin jikkatar fararen hula, ciki har da wanda ya ƙona wani sansanin Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a cikin watan Mayu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 46. Netanyahu da kansa ya ce harin "babban kuskure ne."

An yi jinyar ɗaruruwan mutanen da suka jikkata sakamakon harin, ciki har da munanan ƙone-ƙone, ƙwararru a MDD sun fusata da harin. A farko watan Fabrairu, kusan hare-haren Isra'ila huɗu sun kashe fararen hula aƙalla 95.

Kimanin rabin mutanen da harin ya shafa yara ne, kuma ƙungiyar ƙare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana harin da ''take doka'' kana ta ƙara da cewa, ''sojojin Isra'ila na ci gaba da take dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, tare tarwatsa iyalai baki ɗaya ba tare da samar musu da kariya ba.''

Ƙarya: "Yawancin Amurkawa ba su yarda da wannan farfagandar Hamas ba, suna ci gaba da goyon bayan Isra'ila," in ji shi.

Gaskiya: Ikirarin Netanyahu na cewa "yawancin Amurkawa" suna goyon bayan yaƙinsa a Gaza ba gaskiya ba ne.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa wani kaso mai tsoka na Amurkawa ko dai ba su amince da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ba ko kuma suna da shakku kan abubuwan da ke faruwa a kan yaƙin Isra'ila a Gaza.

Binciken kamfanin Gallup na wata-wata ya gano cewa yayin da aka sami raguwar rashin amincewa da yaƙin, an samu ragin kaso 7 daga kashi 48 cikin100 a watan Maris zuwa Yuli, don haka har yanzu akwai ragi kaso mai yawa daga al'ummar Amurka wadanda suke da shakku kan yakin.

AP