"Dakatar da bayar da kudade ga hukumar UNRWA mai kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira saboda zargin da ake yi wa wasu ma'aikatanta, zai yi illa ga Falasdinawa," in ji Ma'aikatar Wajen Turkiyya, tana mai cewa hukumar tana tallafa wa miliyoyin mutane. /Hoto: TRT World

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta nuna damuwa game da matakin da wasu kasashe suka dauka a baya bayan nan na dakatar da bayar da tallafin kudi ga Hukumar Kula da Falasdinawa 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA).

"Hukumar UNRWA tana aiki cikin mawuyacin hali inda take biyan bukatun miliyoyin Falasdinawa 'yan gudun hijira," a cewar wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ranar Lahadi.

Da take bayani game da mawuyacin yanayin da UNRWA take gudanar da ayyukanta, ma'aikatar harkokin wajen ta bayyana cewa tun ranar 7 ga watan Oktoba, an kashe ma'aikata fiye da 150 na hukumar a Gaza, abin da ke nuna hatsarin da mutanen da ke taimaka wa Falasdinawa suke fuskanta.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kira ga kasashen su sake nazari game da matakinsu na dakatar da bayar da tallafin kudi ta Hukumar UNRWA mai Kula da Falasdinawa 'Yan Gudun Hijira, tana mai cewa "dakatar da bayar da kudade ga hukumar UNRWA mai kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira saboda zargin da ake yi wa wasu ma'aikatanta, zai yi illa ga miliyoyin Falasdinawa."

Kasashen da suka dakatar da bai wa UNRWA tallafi

An dauki matakin dakatar da bayar da tallafi ga hukumar UNRWA sakamakon zargin da Isra'ila ta yi wa ma'aikatanta cewa suna cikin wadanda suka kai mata hari ranar 7 ga watan Oktoba.

Kasashen da suka dakatar da bayar da tallafin ranar Asabar sun hada da Australia, Birtaniya, Finland, Jamus da Italiya bayan Amurka ta dauki matakin na dakatar da bai wa UNRWA tallafi tun da farko .

Francesca Albanese, wakiliya ta musamman ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinu, ta yi gargadi cewa dakatar da bai wa UNRWA tallafi "ya saba wa" tsarin Kotun Kasa da Kasa da ya bukaci kai kayan agaji Gaza.

TRT World