Fadar White House a ranar Juma’a ta ce Washington za ta gudanar da wani shiri na musamman na tsugunar da manoman Afirka ta Kudu da iyalansu a matsayin ‘yan gudun hijira. / Hoto: Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya saka hannu kan wata doka wadda za ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi, inda Fadar White House ta bayyana dalilan hakan da batun ƙarar da Afirka ta Kudun ta shigar gaban Kotun Duniya kan Isra’ila da kuma rashin amincewarta game da sabon tsarin filaye.

"Muddin Afirka ta Kudu za ta ci gaba da tallafa wa miyagu a fagen siyasar duniya tare da ba da damar kai hare-hare a kan tsirarun manoma da ba su ji ba ba su gani ba, Amurka za ta daina ba da taimakon da take bai wa kasar,” in ji Fadar White House.

Washington ta koka kan shari'ar da Afirka ta Kudu ta gabatar a gaban kotun ICJ, inda ta zargi Isra'ila da kisan kiyashi kan kisan gillar da Tel Aviv ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban Falasdinawa tare da haddasa rikicin bil adama.

Amurka ta bayar da wannan a matsayin wani misali na yadda Afirka ta Kudu ke nuna ta ja daga tsakanin Washington da ƙawayenta.

Haka kuma Trump ya yi Allah wadai da tsaron filaye na Afirka ta Kudu.

Fadar White House a ranar Juma’a ta ce Washington za ta gudanar da wani shiri na musamman na tsugunar da manoman Afirka ta Kudu da iyalansu a matsayin ‘yan gudun hijira.

Ta ce jami'an Amurka za su dauki matakan ba da fifiko wajen bayar da agajin jin kai, da suka hada da karbar baki da kuma sake tsugunar da su ta hanyar shirin shigar da 'yan gudun hijira na Amurka ga ‘yan ƙabilar Afrikaners a Afirka ta Kudu, wadanda galibinsu fararen fata da asalinsu mazauna Holland da Faransa.

TRT World