Trump ya bayar da shawarar mayar da Falasɗinawan Gaza ƙasashe makwabta irin Masar da Jordan

Trump ya bayar da shawarar mayar da Falasɗinawan Gaza ƙasashe makwabta irin Masar da Jordan

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi magana da Sarkin Jordan kuma yana sa ran magana da shugaban Masar game da lamarin.
Trump ya kuma bayyana cewa mayar da su can zai iya zama na wucin-gadi ko kuma na tsawon lokaci. / Hoto: AA

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da shawarar mayar da Falasɗinawan da ke Gaza ƙasashen makwabta kamar Masar da Jordan, wanda wannan wata shawara ce da a baya gwamnatin Biden ta ƙi amincewa da ita.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai gabanin barinsa Los Angeles zuwa Miami, shugaban ya ce ya ɗago da batun ne a lokacin da yake magana ta wayar tarho da Sarki Abdullah II na Jordan haka kuma ya bayyana cewa akwai yiwuwar zai yi magana da Shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi kan wannan batu a ranar Lahadi.

“Na shaida masa (Sarkin Jordan) cewa ina so ka karɓe su dayawa saboda a yanzu ina kallon Gaza baki ɗaya a matsayin wadda ba ta cikin hayyacinta,” in ji Trump. “Ina son (Sarkin Jordan) ya karɓi mutanen”.

“Ina so Masar ta karɓi mutane. Ina sa ran zan yi magana da Sisi gobe. Kuma "Ana magana ne game da mutane miliyan daya da rabi, kuma muna so mu gyara komai. Kun san cikin ƙarni da yawa ana fama da rikice-rikice masu yawa. Kuma ban sani ba, dole ne wani abu ya faru," in ji shi.

A yayin da yake kwatanta Gaza da matsayin wani wuri da “aka rushe,” shugaban Amurkar ya bayyana cewa: “An rushe kusan ko ina kuma mutane na mutuwa a can. Ina ga ya fi kyau na yi magana da wasu ƙasashen Larabawa a gina musu gidaje a wasu wuraren ta yadda za su iya rayuwa cikin zaman lafiya,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Ya kuma bayyana cewa mayar da su can zai iya zama na wucin-gadi ko kuma na tsawon lokaci.

TRT World