Erdogan ya  jaddada cewa wajibi ne kasashe su yi garambawul kan dokokinsu da suka kyale ana kona Alkur'ani mai tsarki.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin cewa Turkiyya ba za ta yi shiru da bakinta ba game da makiya Musulunci da masu nuna wariyar launin fata.

"Kona Alkur'ani laifi ne karara na kiyayya kuma ba za a amince da shi ba da sunan fadar albarkacin baki," in ji Erdogan lokacin taron manema labarai bayan kammala taron G20 karo na 18 a New Delhi ranar Lahadi.

Ya jaddada cewa wajibi ne kasashe su yi garambawul kan dokokinsu da suka kyale ana yin wannan danyen aiki.

Tattaunawa kan F16

A wani batun na daban, Shugaba Erdogan ya ce ya tattauna game da jiragen yaki samfurin F16 yayin da ya yi wata gajeriyar ganawa da takwaransa na Amurka Joe Biden a gefen taron G20.

"Mun tattauna a tsaitsaye da Biden. Kazalika mun tattauna kan batun F16," a cewar Erdogan a taron manema labarai.

Ankara ya bukaci sayen jiragen yakin na F16 da kuma kayan aiki a watan Oktoba na 2021. Yarjejeniyar da aka kulla da ta kai $6b za ta hada da sayen jiragen yaki 40 da kayan sabunta jiragen yaki 79 wadanda tuni suke cikin Jiragen Sojojin Saman Turkiyya. Ma'aikatar Tsaron Amurka ta shaida wa Majalisar Dokokin kasar game da cinikin.

Labari mai alaka: Turkiyya ba za ta lamunci kona Alkur’ani ba: Erdogan

Sai dai wasu manyan 'yan majalisar dokokin sun ce za su bari a sayar wa Ankara jiragen ne bisa wasu sharuda, da suka hada da neman Turkiyya ta amince da Sweden ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO.

Ankara ta dage cewa jiragen yakin za su taimaki ba kawai Turkiyya ba har ma da NATO.

'Dole Sweden ta cika alkawuran da ta dauka'

Shugaban Turkiyya ya ce majalisar dokokin kasar ce za ta yanke hukunci kan bai wa Sweden damar zama mamba a NATO.

"Ba ni ne nake da alhakin hakan ba. Dole sai majalisa ta amince da batun. Kuma dole ne Sweden ta cika alkawuran da ta dauka," in ji shi.

Turkiyya ta jaddada cewa bukatar Sweden ta zama mamba a NATO da matakin Turkiyya na sayen jiragen yaki samfurin F16 daga Amurka batutuwa ne da ba su da alaka.

Dukkan shugabannin G20, idan ban da shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping, sun halarci taron na kwana biyu da aka yi a New Delhi mai taken "Duniya Daya, Iyali Daya, Makoma Daya."

AA