Maryam Alwan ta gane komai ya zo karshe bayan da 'yan sandan New York sun kama ta tare da sauran masu zanga-zanga a Jami'ar Columbia, suka loda su a motocin bas tare da tsare su na tsawon awanni.
Amma a yammacin da ya biyo baya, alibar ta jami'a ta samu sakon email daga jami'ar. An dakatar da Alwan da sauran wasu daliban bayan an kama su a wajen zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza, wata sabuwar dabara da manyan makarantu a Amurka ke amfani da ta don daƙushe zanga-zangar adawa d ayakin da Isra'ila ke yi a Gaza da dalibai ke gudanarwa.
Bukatun daliban sun zama wani bangare na jigon zanga-zangar, inda dalibai da malaman jami'a ke naman da a yi musu afuwa. Abinda ba a sani ba shi ne ko mahukunta za su soke tuhumar sannan kuma shin wannan laifi zai bi su har girman su ko kuwa a'a.
Yanayin dakatar da dalibai yana sauya wa daga wata makarantar zuwa wata. A Jami'ar Columbia da Kwalejin Barnard dake da alaka da ita, mata, an kama Alwan da gwamman wasu a ranar 18 ga Afrilu, kuma nan da nana aka hana su shiga azuzuwa da ma jami'ar gaba daya, sun gaza zuwa da kan su ko su wakilta wani, haka ma ba sa samun damar zuwa wajen cin abinci na makarantar.
Ana ta tambaya game da makomar karatunsu. Shin z aa ba su damar rubuta jarrabawar karshe? Yaya batun taimakon kudi? Kammala karatu? Columbia ta ce za a samu sakamako bayan kwamitin ladabtarwa ya zauna, amma Alwan ta ce ba a ba ta rana ba.
"Wannan yanayi ne mai bakantawa," in ji Alwan, dalibar adabi da zamantakewar al'umma.
Abinda ya faro a Columbia ya zama wani takun saka a fadin kasar tsakanin dalibai da jagorori kan nuna adawa da yaki da takaita fadin albarkacin baki.
A kwanaki 10 da suka gabata, an kama daruruwan dalibai, an dakatar da su tare da saka sunayensu a jerin wadanda za a iya kora daga jami'a a wasu wuraren ma an kore su daga makarantun ciki har da Jami'ar Yale, Jami'ar Southern California, Jami'ar Vanderbilt da Jami'ar Minnesota.
Barnard, kwalejin nazarin 'yanci ta Jami'ar Columbia, ta dakatar da sama da dalibai 50 da aka kama a ranar 18 ga Afrilu tare da korar su ta karfi daga gidajen kwana na jami'ar, kamar yadda daliban suka bayyana a tattaunawar da aka yi da su da jaridar Columbia Spectator, wadda ta samu wasu bayanai na cikin gida.
A ranar Juma'a, Baranard ta sana da sun cimm amatsaya kan ba wa kusan dukkan su damar dawo wa makaranta. Sanarwar da kwalejin ta fitar ba ta bayyana adadin wadanda aka janye wa dakatarwar ba.
A daren da aka yi kamen, dalibar Barnard Maryam Iqbal ta yada wani hoto a shafin X da ke dauke da sakon email da shugaban tsangayarsu ya yi mata yana cewa ta dawo dakinta karkashin kulawar jami'an tsaro kafin a kore ta.
Sakon email din ya ce "Za a ba ki mintuna 15 ki tattara komatsanki da kike bukata."
Sama da dalibai 100 na Barnard da Columbia ne suka yi tattakin "Goyon Baya a Dalibanmu" a makon da ya gabata inda suka la'anci kama daliban tare da kira da a janye dakatarwar da aka yi musu.
Har yanzu Columbia na kokarin cire antin da aka saka a bayan makaratar inda ake shirin gudanar da taron yaye dalibai a ranar 15 ga watan Mayu.
Daliban na neman jami'ar ta yanke hulda da kamfanonin da ke da alaka da Isra'ila tare da tabbatar da an yi afuwa ga daliban da malaman da aka kama saboda znaga-zanga.
Ana ci gaba da tattaunawa da daliban da ke zanga-zanga, in ji Ben Chang, kakakin Jami'ar Columbia. "Muna da namu bukatun; suna da nasu," in ji shi.
A ce daliban kasa da kasa na fuskantar dakatarwa, akwai tsoron su yi asarar visa da izi nin zaman su, in ji Radhika Sainath, wata lauya a ofishin Kare Falasdinawa da ta taimakawa daliban Columbia shigar da korafi a Hukumar Korafe-Korafe ta Tarayya don kalubalantar jami'ar a ranar Alhamis. ta zargi jami'ar Columbia da gaza yin abinda ya kamata don kare daliban Falasdin.
Sainath ta ce "Matakin ladabtarwar ba na ukuba ba ne kawai, har ma da nuna rashin damuwa da mutane."
A makon da ya gabata an kama sama da dalibai 40 a wajen zanga-zanga a Jami'ar Yale, ciki har da babban dalibi Craig Birckhead-Morton.
Yana shirin kammala karatu a ranar 20 ga watan Mayu, amma ya ce har yanzu jami'ar ba ta fada masa ko za a miƙa shi ga kwamitin ladabtarwa ba, yana da damuwa kan ko ba za a ba shi sakamakon kammala karatu, sannan ko yana fuskantar hatsarin fara digiri na biyu a Columbia.
"Makarantar ta yi iya kokarinta wajen yin biris da mu ba tare da fada mana makoma ba." in ji Birckhead-Morton, dalibin tarihi.
A fadin kasar ta Amurka, jagororin manyan makarantu na ta gwagwarmayar daidaita 'yancin bayyana ra'ayi da tafiya tare da kowa. Mahukuntan Amurka na ikirarin wasu masu zanga-zanga sun nuna kalaman nuna kyama, nuna kyama ga Yahudawa ko goyon bayan Hamas.
Bukukuwan watan Mayu na kara matsa lamba don kawo karshen zanga-zangar. Jami'an Jami'o'i na cewa kame da dakatarwa ne matakin karshe, kuma suna fara bayar da gargadi kain su sa a tarwatsa masu zanga-zangar.
Jami'ar Vanderbilt da ke Tennesseta korar dalibai kawai bisa laifin da ya shafi zanga-zanga kan rikicin Isra'ila da Falasdin, kamar yadda Cibiyar Nazarin fahimtar Gabas ta Tsakiya ta sanar.
A ranar 26 ga Maris sama da gwamman dalibai ne suka yi zaman dabaro a gaban ofishin shugaban jami'ar tsawon awanni inda aka kira 'yan sanda suka kama da yawa daga cikin su.
Daga baya kuma aka sanar da korar dalibai uku, da saka sunayen wasu 22 a jerin wadnada za a iya kora daga makaranta.
A budaddiyar wasikar da suka aikewa Shugaba Jami'ar Daniel Diermeier, sama da farfesoshi 150 sun soki yadda jami'ar ta dinga murkushe dalibai.
Freshman Jack Petocz dan shekara 19, na daga cikin wadanda aka kora, amma ya dinga zuwa azu sakamakon daukaka hukuncin da ya yi uwa sama. An kore shi ta karfi daga gidan kwanan dalibai tare da hana shi zama a cikin makarantar.
Petocz ya ce yin zanga-zanga a manyan makarantu ne ya taimaka masa shiga Vanderbilt tare da samun tallafin karatu ga masu fafutuka.
Binciken da ya yi ma ya shafi masu shirya tattaki a kauyukan Florida da suke adawa da Gwamna Ron DeSantis da yake nuna adawa da LGBTQ.
"Vanderbilt ya kaunaci hakan," in ji Petocz. "Abin takaici, wannan yabo da kyautayi na zuwa karshe a lokacin da ka fara nuna goyon baya ga 'yancin Falasdinawa."