Dubban mutane ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon wadannan cututtuka. Hoto/Reuters

Matsalar sauyin yanayi ta kawo cikas wurin yaki da ake yi da cututtuka masu yaduwa, kamar yadda shugaban Asusun Yaki da AIDS da Tarin Fuka da malaria ya bayyana.

Tsare-tsare na kasa da kasa domin yakar cututtuka sun farfado matuka bayan annobar korona wadda ta yi matukar illa, kamar yadda asusun ya bayyana a rahoton da ya fitar a ranar Litinin.

Sai dai kalubalen da ke karuwa na sauyin yanayi na nufin akwai yiwuwar duniya ta kasa kawar da cutar AIDS da Tarin Fuka da malaria zuwa 2030 ba tare da wasu “matakai na musamman” ba, in ji Peter Sands, babban daraktan asusun.

Alal misali, malaria na yaduwa a sassan Afirka wadanda a baya sun yi sanyi sosai ga sauro ya rayuwa.

Bala’o’in sauyin yanayi da dama da suka hada da ambaliyar ruwa na jawo matsaloli bangaren kiwon lafiya da raba jama’a da muhallansu da kuma kawo cikas wurin yi wa jama’a magani.

A kasashe kamar Sudan da Ukraine da Afghanistan da Myanmar tafiya ga al’ummomi wadanda suka fi rauni ya kasance lamari mai wahala saboda rashin tsaro.

Ba a cire rai baki daya ba

Sai dai duk da haka akwai kyakyawar fata. Alal misali, a 2022, an yi wa mutum miliyan 6.7 maganin cutar TB a kasashe wadanda asusun ke zuba jari, inda aka yi wa mutum miliyan 1.4 a shekarar da ta gabata.

Haka kuma asusun ya taimaka wurin samar da magungunan masu cutar HIV ga mutum miliyan 24.5 da kuma ba su gidan sauro miliyan 220.

Sands ya kara da cewa abubuwan da ake da su na kiyayewa da kuma gano cututtuka na sa ana kyakyawan fata.

A wannan makon, akwai wata babbar tattaunawa a kan TB a taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya inda ake kira kan a kara mayar da hankali kan cututtukan.

Asusun na duniya ya fuskanci caccaka daga wasu daga cikin masana kan tarin fuka sakamakon kin bayar da isassun kudi domin yakar cutar, wadda ita ce ta fi kisa a cikin cututtuka uku wadanda kungiyar ta fi mayar da hankali a kai.

TRT World