Majiya daga Yeman ta bayyana cewa Saudiyya da 'yan Houthi sun cimma matsaya kan tsagaita wuta na tsawon watanni shida/Hoto (Reuters)

Wata tawagar Saudiyya ta je babban birnin kasar Yemen domin yiwuwar kulla sabuwar yarjejeniya da 'yan tawayen Houthi da Iran ke goyon baya, wadanda ke rike da ikon birnin, a cewar jami’an diflomasiyya.

Kafofin yada labaran Houthi sun nuna jagoran siyasa na kungiyar, Mahdi al Mashat yana musabaha tare da ganawa da manyan jami'an diflomasiyyar Saudiyya, ciki har da jakadan masarautar a Yemen, Mohammed Al Jaber.

Jami'an Saudiyyan sun je "Sanaa ne don tattauna hanyoyin ci gaba da samar da zaman lafiya a Yemen," in ji wani jami'in diflomasiyyar Yemen mazaunin yankin Gulf, bayanin da wani jami'in diflomasiyya na biyu ya tabbatar.

Ziyarar tawagar na zuwa ne kasa da wata daya bayan taimakon da China ta yi na shiga tsakani wajen samar da maslaha ta ba-zata tsakanin Saudiyya da Iran.

Yarjejeniyar da ta kara kwarin gwiwa da fatan samun ci gaba wajen kawo karshen rikicin kasar Yemen da ya lakume rayukan dubban mutane, tare da janyo abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira yanayi mafi muni da mutane suka shiga a duniya.

Manyan jami'an diflomasiyyar Saudiyya da na Iran sun gana a ranar Alhamis din da ta wuce a China, inda suka yi alkawarin yin aiki tare don samar da "tsaro da kwanciyar hankali" a yankinsu mai cike da tashin hankali.

A ranar Asabar din da ta wuce ne kuma masu shiga tsakani na kasar Oman suka isa birnin Sanaa.

A shekarar 2014 ne mayakan Houthi suka kwace iko birnin Sanaa, lamarin da ya haifar da rikici tsakanin gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita, wacce gamayyar sojoji karkashin jagorancin Saudiyya ke goyon baya na tsawon shekaru takwas.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da aka sanar kusan shekara guda da ta gabata ta rage yawan tashin hankalin da ake fama da shi a Yemen, kuma har yanzu ana matukar mutunta hakan duk da cewa a hukumance a watan Oktoba yarjejeniyar ta zo karshe.

TRT World