Jami'an tsaro da tawagogin likitoci sun isa bayan harin da sojojin Isra'ila suka kai a Lebanon. / Hoto: AA

Laraba, 25 ga Satumban 2024

1404 GMT — Akalla mutum 51 ne suka mutu sannan wasu 223 suka jikkata sakamakon sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon, in ji Ministan Lafiya na Lebanon Firass Abiad yayin wani taron manema labarai.

1410 GMT Mutum 90,000 sun rasa matsugunansu a Lebanon tun ranar Litinin: MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 90,000 ne suka rasa matsugunansu a Lebanon cikin wannan mako, yayin da Isra'ila ke kai hare-hare kan wuraren da ta ce na kungiyar Hezbollah ne a fadin kasar, sannan kuma kungiyar ta Lebanon ta kai hari kan Isra'ila.

Tun daga ranar Litinin, Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta rubuta "sabbin mutane 90,530 da suka rasa matsugunansu", in ji wata sanarwa.

Daga cikin su, "da yawa daga cikin mutane sama da 111,000 da suka rasa matsugunansu ne tun watan Oktoba... na iya zama sun sake rasa matsugunan nasu a karo na biyu", in ji wata sanarwa da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, tana mai nuni da fara rikicin kan iyakokin kasar tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

1356 GMT — Amurka da ƙawayenta na aiki "ba gajiyawa ba" don guje wa barkewar yaki gadan-gadan a Lebanon

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce hadarin da ke tattare da ta'azzarar yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya ya yi matukar yawa, kuma Washington da kawayenta suna aiki tukuru domin kauce wa barkewar yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah ta Lebanon.

"Muna haduwa a lokacin da ake cikin tashin hankali," in ji Blinken a farkon wata ganawa da manyan jami'ai da ministocin kungiyar hadin kan yankin Gulf (GCC) a birnin New York.

Ya kara da cewa, "Hadarin ci gaba da ta'azzara a yankin na da matukar yawa. Mafi kyawun amsa ita ce diflomasiyya, kuma hadin kanmu na da matukar muhimmanci wajen hana ci gaban ta'addanci."

TRT World