Amurka za ta aika jiragen yaki na ruwa da na sama kusa da Isra’ila.  / Photo: Reuters / Photo: AP

Amurka za ta aika jiragen yaki na ruwa da na sama kusa da Isra’ila

Amurka za ta aika jiragen yaki na ruwa da na sama kusa da Isra’ila don nuna goyon bayanta, a cewar Sakataren Tsaro Lloyd Austin, inda Washington ta yi amannar cewa hare-hare masu muni da Hamas ta kai ta yi su ne da nufin rusa ƙoƙarinta na sasanta tsakanin Isra’ila da Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

17:30 GMT - An zargi Isra’ila da kashe wani dan Hezbollah a harin da aka kai kan iyaka

Wani hari da Isra’ila ta kai kan wata hasumiyar sintiri ta Labanon ya yi sanadin kashe wani ɗan ƙungiyar Hezbollah a ranar Litinin.

A cewar ƙungiyar a yayin da ake ci gaba dakai hare-haren bayan da wasu mayaƙan Falasdinu suka yi ƙoƙarin kutsawa Isra’ila daga Labanon.

Rundunar sojin Isra’ila ya ce sojojinta sun kashe wasu mayakan da ake zargi da dama, wadanda suka shiga yankinta daga Labanin kuma helikwaftanta yana shawagi da sa ido a yankin.

17:23 GMT

Hamas ta yi barazanar kashe ‘yan Isra’ilan da take garkuwa da su saboda hare-haren da ake kai wa Gaza.

1406 GMT — Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa za su yi taro a kan Gaza ranar Laraba: Arab League

Ministocin Harkokin Wajen Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa za su yi wata ganawa a ranar Laraba don tattaunawa kan "Kutsen Isra'ila a Zirin Gaza", kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

Taron "wanda ba kasafai ake irin sa ba" da za a yi a birnin Alƙahira na Masa zai yi duba ne kan "hanyoyin da za a ɗauki matakin siyasa a tsakanin ƙasashen Larabawa da ma ƙasashen duniya," a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza bayan harin da aka kai mata ranar Asabar, kamar yadda mataimakin shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Larabawan Hossam Zaki ya faɗa a wata sanarwa.

1407 GMT — Jamus ta dakatar da ayyukan jin kai ga Falasdinawa

Jamus ta dakatar da ayyukan jin kai na wucin gadi ga Falasdinawa da hukumomin Falasdinu sakamakon harin da Hamas ta kai wa Isra'ila, a cewar wata mai magana da yawun Ma'aikatar Tattalin Arziki da Hadin Kai da Cigaba ta ƙasar.

A yanzu za a sake yin sabon nazari kan shirye-shiryen da kuma sanar da matsayar da aka cimma, kamar yadda Katharian Koufen ta shaida wa manema labarai a Berlin.

Ta ce kusan dala miliyan 131.85 aka yi alkawarin kashewa nan ba baɗi a yarjejeniyar hadin gwiwa ta cigaba.

Jamus ta dakatar da ayyukan jin kai ga Falasdinawa. Hoto: Others

1345 GMT — Faransawa takwas sun mutu ko sun ɓata ko an yi garkuwa da su a harin Hamas - Dan Majalisa

Dan majalisar dokoki mai ra'ayin riƙau Meyer Habib, wanda yake wakiltar al'ummar Faransa da ke zama a ƙasashen waje na yankin Meditareniyan da suka haɗa da Isra'ila, ya ce "aƙalla Faransawa takwas ne aka yi amannar ko dai sun ɓata ko sun mutu ko kuma ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su," a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

Labari mai alaka: An kashe 'yan Isra'ila sama da 600, an jikkata 2,000

Amma ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta tabbatar da mutuwar mutum biyu ne kawai a wata sanarwa.

"Faransa tana alhinin mutuwar ɗan kasarta na biyu da ya rasa ransa a hare-haren ta'addancin da Hamas ta kai wa Isra'ila," a cewar ma'aikatar.

"Muna ci gaba da ƙoƙarinmu na fayyace halin ƴan ƙasarmu da har yanzu ba a ji ɗuriyarsu ba ke ciki."

0100 GMT 0200 — Martanin Isra'ila a kan Gaza zai 'sauya' Gabas ta Tsakiya — Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce martanin Isra'ila kan Hamas a Gaza zai "sauya Gabas ta Tsakiya".

Yana magana ne ga rukunin magajin garin garuruwan da ke kan iyakar kudancin kasar waɗanda hare-haren ranar Asabar ya shafe su, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa. Sai dai bai yi ƙarin bayani ba a kan hasashen nasa.

Hamas ta ƙaddamar da harin da ta kira Operation Al Aqsa Flood a kan Isra'ila da safiyar ranar Asabar, inda suka harba rokoki. Ta ce harin shammata martani ne kan afka wa Masallacin Ƙudus da kuma ci gaba da mamayar Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ke yi.

A martanin da ta mayar, rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da harin da ta kira Operation Swords of Iron. Ta kai hare-hare kan wurare 500 cikin dare a Gaza, waɗanda ta ce na ƙungiyar Hamas da ƙungiyoyi masu da'awar Jihadi ne.

0100 GMT 0200 — Isra'ila ta yanke ruwa da wuta da kai abinci Gaza

Israi'ila ta sanar da yi wa baki ɗayan Gaza ƙawanya a yayin da faɗa ke ci gaba da ruruwa tsakaninta da Ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas.

"Na ba da umarnin a yi wa Gaza ƙawanya ruf," a cewar Ministan Tsaron Yoav Gallant bayan wani taron tattaunawa kan lamarin, a cewar shafin jaridar Times of Israel.

"Ba za mu samar musu da wutar lantarki da abinci da man fetur ba, an rufe Gaza ruf," Gallant ya ƙara da cewa.

Ministan Makamshi na Israi'ila Katz shi ma ya bayar da umarnin katse hanyoyin samar da ruwan sha zuwa Gaza," kamar yadda mai magana da yawunsa ya fada a wata sanawa.

Umarnin Katz na zuwa ne jim kadan bayan umarnin Gallant na rufe Gaza ruf, wacce ke samun kusan kasi 10 cikin 100 na ruwan shanta daga Isra'ila.

Da safiyar ranar Litinin, rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kai hare-hare wurare 500 kan Gaza cikin dare, tana mai ikirarin cewa wuraren maɓoyar Hams da masu ikirarin jihadi ne.

Ƙungiyar Hamas mai cibiya a Gaza ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila a ranar Asabar, ta hanyar harba rokoki. Ta ce ta yi harin ban mamakin ne a matsayin martanin ga kutsen da Isra'ila ke yi wa Masallacin Ƙudus da kuma mamayar Yammacin Kogin Jordan da ke ƙaruwa.

Ita ma Isra'ila ta mayar da martanin ta hanyar kai hare-hare kan Hamas a Zirin Gaza, inda Falasɗinawa 493 suka mutu sannan aƙalla 2,751 suka jikkata.

Aƙalla ƴan Isra'ila 700 aka kashe kuma fiye da 2,300 suka jikkata a yaƙin, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Isra'ila.

0100 GMT — Tarayyar Turai za ta yi taro

Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai za su yi wani taron gaggawa a ranar talata a kan lamarin Isra'ila da Gaza bayan da ƙungiyar mayaƙan sa kai ta Hamas ta ƙaddamar da wani hari na ban mamaki, a cewar shugaban harkokin wajen EU Josep Borrell.

"A gobe zan yi wani taron gaggawa da Ministocin Harkokin Wajen EU don duba kan abin da ke faruwa a Isra'ila da ma yankin," kamar yadda Borell ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Litinin.

Borrell da wasu ministocin EU a yanzu haka suna ƙasar Oman inda suke halartar wata tattaunawa da ka daɗe da shirya yin ta da ƙasashen yankin Gulf da kuma Hukumar Hadin Kan Ƙasashen Yankin Gulf ɗin.

Ana ci gaba da ruwan bama-bamai a tsakanin Isra'ila da Hamas

Wani mai magana da yawun Borrell a Brussels, Peter Stano, ya ce za a yi tattaunawar ta EU ne ta bidiyo.

EU ta yi Allah wadai da harin da ba a taɓa ganin irinsa ba daga mayaƙan sa kan masu tsananin kishin Musulunci da ya jawo hare-haren martani kan Gaza da Isra'ila ta kai.

Litinin 9 ga watan Oktoba, 2023

1007 GMT — Rasha da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa na son a daina zub da jini

Moscow da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa za su yi aiki don "dakatar da zubar da jini" a Israi'la da Gaza, kamar yadda ministan harkokin wajen Rasha ya faɗa bayan wata ganawa da shugaban Ƙungiyar Larabawa Ahmed Aboul Gheit.

Gheit ya je Moscow ne don tattauna bayan da gagarumin harin da ƙungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila.

"Na tabbata cewa Rasha da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa za su haɗa kai fiye da komai don dakatar da zubar da jinin," a cewar Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov. Lavrov ya ce ya zama wajibi "a yi gaggawar dakatar da rikicin, a warware matsalar tare da fararen hula... a kuma gano dalilin da ya sa har yanzu ba a samo mafita kan rikicin Isra'ila da Falasdinu ba."

Ya ce Moscow da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa za kuma su yi aiki "da ƙasashen da ke da sha'awar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya."

Gheit, wanda tsohon ministan harkokin waje ne a Masar, ya ce ya yi Allah wadai "da rikicin daga kowane ɓangare."

"Muna neman a samar da wasu tsare-tsaren siyasa da kuma mafita ta adalci a rikicin Falasɗinu da Isra'ila," ya ce.

Litinin 9 ga watan Oktoba, 2023

09:30 GMT — Isra'ila ta kashe iyalai 15 na Falasdinawa a Gaza

Sojojin Isra'ila sun yi wa mutum 15 daga iyalai daban-daban "kisan gilla" a yankin Gaza inda suka bi su gida-gida suna kashe su a yayin da adadin mutanen da aka kashe a yankin ya kai kusan 500, a cewar jami'an Falasdinu.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu ta ce kawo yanzu an kashe Falasdinawa akalla 493 sannan aka jikkata 2,751 a ci gaba da hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza.

Wata Bafalasdinuwa a yayin da ake cir ta daga wani gini bayan harin da Isra'ila ta kai  musu./Hoto: Reuters

0855 GMT — Rikicin Isra’ila da Falasdinawa ya raba mutum 123,538 da muhallansu a Zirin Gaza

Karuwar rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa ya raba mutum 123,538 da muhallansu a Zirin Gaza, kamar yadda ofishin da ke kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

Kungiyar Hamas da ke Gaza ta kaddamar da wani samame mai suna “Operation Al-Aqsa Flood” a ranar Asabar, inda ta kutsa cikin Isra’ila tare da harba makaman roka.

Kungiyar ta ce ta kaddamar da wannan harin domin mayar da martani kan yadda dakarun Isra’ila ke yawan kai samame Masallacin Birnin-Kudus a Gabashin Birnin Kudus.

Haka kuma Hamas din ta koka kan yadda ake samun karuwar rikici tsakaninsu da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna a Gaza.

0745 GMT — Mayakan Falasdinawa kusan 1,000 suka kutsa kai yankin Isra'ila

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa kusan mayakan Falasdinawa 800 zuwa 1,000 suka kutsa cikin Isra’ila ta hanyoyi 80 wadanda ke kan iyaka da Gaza.

Wannan na zuwa ne bayan wani babban jami’in Isra’ila a ranar Lahadi ya tabbatar da an samu “babbar gazawa a leken asiri” a makonnin da suka gabata wanda a cewarsa ya jawo babban rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Zuwa yanzu mutum 436 suka mutu a Gaza sakamakon harin da Isra’ila ta kai – daga ciki har da yara 91 da mata 61, in ji Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza.

Hukumomi a Isra’ila kuma sun bayyana cewa kusan mutum 700 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin mayakan Hamas.

0718 GMT Ana ci gaba da rikici tsakanin dakarun Isra’ila da mayakan Hamas a wurare kusan takwas da ke kusa da Gaza, kamar yadda sojoji suka bayyana.

“Muna ci gaba da yaki. Akwai wurare tsakanin bakwai zuwa takwas a kusa da Gaza wadanda muke da mayaka inda suke fada da ‘yan ta’adda,” in ji mai magana da yawun soji Richard Hecht a tattaunawarsa da manema labarai, kwanaki biyu bayan kungiyar ta Falasdinawa ta kaddamar da harin ba-zata kan garuruwan Isra’ila da ke kusa da Gaza.

“Mun dauka zuwa jiya za mu samu cikakken iko. Amma muna sa rai zuwa karshen yau za mu samu.”

A cikin dare, Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama fiye da 500 da amfani da makaman atilari inda aka kashe gomman Falasdinawa.

TRT Afrika da abokan hulda